KANO: Hadarin mota ya kashe mutum 18 da wasu yan gida daya su 6

Hadarin mota ya kashe mutum 18 da wasu 6 yan gida daya a Kano

Daga Muryoyi

Hadarin mota ya kashe akalla mutum 18 da wasu mutum 6 yan daki daya a karamar hukumar Doguwa dake jihar Kano.

Muryoyi ta tattara rahoton cewa hadarin ya rutsa da iyalin wani

- Advertisement -

Malam Bashir Doguwa wanda ya kwashi iyalinsa su 6 daga garin Doguwa zasu je ziyaratar daya diyarsa Firdausi Bashir a makarantar Sakandaren mata ta First Lady Secondary School dake Dambatta wacce take kan rubuta jarabawar NECO

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Kano Zubairu Mato ya ce hadarin ya faru ne a ranar Juma’a 23 ga watan Yuni da muke ciki a daidai gadar Shiburu inda motar tasu kirar Volkswagen Sharon ta afka rafi sakamakon karyewa da gadar tayi saboda ambaliyar ruwa.

Wani da abun ya faru a gaban idonsa ya shaidawa majiyar Muryoyi cewa dreban bai fahimci gadar ta karye ba sai da ya zo gab, wajen kokarin kaucewa sai motarsu ta afka rafi kuma nan take duka fasinjoji 18 dake ciki suka mutu.

Iyalan Malam Bashir 6 dake cikin motar sun hada da shi kansa Malam Bashir Doguwa, da Malami Gidan Tanimu Doguwu, da Safiya Mukhtar Doguwu, da Shashida Bashir me goro Doguwu, da Fatima rabi u me goro Doguwu, da Uzairu Bashir me goro Doguwu, dukansu iyalan margayin kuma yan garin karama hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Muryoyi ta ruwaito tuni akayi jana’izar duka mamatan washe gari ranar Asabar.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: