Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKIDINAFAS: Komai yawan haramun bata kawo wadatar zuci –Wasagu

KIDINAFAS: Komai yawan haramun bata kawo wadatar zuci –Wasagu

Daga Shehu Usman Abdullahi Wasagu

A duk lokacin da aka nuno yan kidnafin zaka gansu a cikin kamanu mafi muni, alamun yunwa da rashin suturar kirki bayan kantar datti a jikin su, wasun su da suma a yamutse.

Anya kuwa miliyoyin kudaden fansa da ake basu na isa hannun su ko akwai wasu da ke a gefe suna turo su?. Waton kura da shan bugu gardi da kwasar kudi.

Ko kuwa tsabar Allah ya-isan mutane ne da tsinuwar Allah da mala’kun sa ke biyar su.

- Advertisement -

Ko kuma duka biyu din, ga tsinuwar Allah da mala’ikun sa da Allah ya-isan jama’a da kuma harkar Kura da shan bugu gardi da kwasar ganima.

Darussa: Cin amanar jama’a yana gadar da wulakanci tun a nan duniya balan tana kiyamar Allah.

Kuma babu wanda zai dauki wannan hanyar ta kidnafin ko taimaka musu da bayanai ko da kayan aiki, sai Allah ya walakan ta shi ya tozar ta shi a duniya da kiyama.

Sannan, komai yawan haramun bata kawo wadatar zuci wanda shine asalin wadata. Mu wadatu da dankadan da muke samu mu roki Allah albarka.

Allah ya tarwatsa Yan kidnafin da duk wani mai taimaka musu. Ya bamu zaman lafiya mai dorewa.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: