Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKo kai ne ka zama shugaban kasa yau sai ka zama abun...

Ko kai ne ka zama shugaban kasa yau sai ka zama abun tausayi indai ka samu irin mutanen dake kewaye da Buhari –Sheikh Daurawa

Daga Muryoyi

Fitaccen Malamin addinin musulunci a Nigeria, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga jihar Kano ya fasa kwai dangane da irin kalubalen da malamai ke fuskanta idan suka fadawa shugaba Muhammadu Buhari gaskiya, malam ya ce

“In kazo zaka ga Shugaba kasa an dinga yi maka wuru-wuru kenan sai an kore ka, duk zuwan da muke yi mu bada shawara sai da akayi wuru-wurun da aka hana mu zuwa.”

“Ko kuma ace mai zaka fada? Wallahi da, duk wata Uku sai an kwashemu malamai mun je mun zauna da shugaban kasa, amma wallahi ina jin yanzu kusan shekara daya da rabi an hana mu zuwa.”

- Advertisement -

“Wani zuwa da mukayi ma na karshe wani wulakanci da akayi mana, muna hotel muka zo duk dakunan mu duk an rufe su. Key [makullai) din da suka bamu ashe na kwana dai-dai ne… muka zo duka makullanmu suka ki bude dakunan. Muka kira limamin da yake yiwa shugaban kasa sallah wallahi kuka ne kawai bai yi ba.”
“Yace haka suke idan mun gayyato malamai wulakanta su suke yi. Saboda kada su dawo. To haka akeyi a rufe mutum. Kai kana nan kana la’antarsa wadanda suka kewayeshi wani yayi tsafi, wani ya sa kaza, wani ya kai laya, wani ya rufe baki, wani ya canza takarda wani signature (sa hannun) sa, wani yayi kaza… haka fa akeyi”

“Sai ka je kusa wallahi [zaka gani], kuma duk wanda zai fadi gaskiya wallahi in yaganka [Buhari] sau daya ka fadi [mashi] gaskiya ba zasu kara bari ka ganshi ba.”

“Ko su bata ka a gurinsa su ce kai mutumin banza ne, ko kuma su hada ka da wane ace ai da wane kuke tare su ce ai kai dan siyasa ne wata siyasa kake yi ko kai dan wata jami’iyya ce shikenan sai a kore ka daga gurinsa.”

“Wani sarki yake fada mini sau 4 yaje fada [fadar shugaban kasa] yana so yaga shugaban kasa amma wallahi bai ganshi ba, sai [su] a aje shi sai yayi awa 4 sai ace [shugaban kasa] ya ce ba zai ganka ba kuma [Buhari] bai sani ba wallahi.”

“To irin wadannan ne Annabi S.A.W yace in Allah yana son ka tsira sai ya kewayeka da mutanen da suna tuna maka in ka manta.
Suna gyara maka in kayi kuskure,
Suna karfafa maka guiwa in ka dauko daidai.” Amma in ka rasa wadannan toh shugabanci bashi da wani amfani.

“Ko kai ne ka zama shugaban kasa yau sai ka zama abun tausayi indai irin wadannan mutanen ne suka kewaye ka. Kuma iri daya ne fa. In ka kori wadannan ka kawo wadansu su ma kansu zasu zo su gina. To ashe mune matsalar kullum ina gaya mana mune matsalar”

“Akwai ranar da muka je da malamai, Malam Taju Allah ya saka masa da alkhairi yayi wa shugaban kasa maganganu masu dadi, yace ranka ya dade [Buhari] kaji tsoron Allah, Allah zai tsaida kai a gabansa yayi maka tambaya, yace EFCC da ka kafa, itama tana bukatar ka sake kafa mata EFCC, wallahi sai shugaban kasa yace la haula wala quwwata illa billah,  sai gashi abunda malam Taju din ya fada shi ya tabbata.”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: