Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKo kinsha maganin mata idan har baki kiyayi yin wadannan abubuwan ba...

Ko kinsha maganin mata idan har baki kiyayi yin wadannan abubuwan ba to da sauranki

Yar’uwa ko kinsha maganin mata idan har baki iyar tafiyar da rayuwan gidan aurenki ba to da sauranki

Daga Muryoyi

Assalamu Alaikum Muryoyi, Sunana Hauwau Sulaiman Lere. Ina so ne in danyi tsokaci akan wani abu da naga yana faruwa a groups dinmu na mata a “Social media” da kuma kira ga yan’uwana mata akan mu gyara please.

Mostly groups da pages na mata a social media zaku ga yan’matane, Matan Aure da kuma Zawarawa most especially facebook groups. A gaskiyan magana akwai abunda matan aure ke yi wanda idan an duba ta fuskan addini bai kamata ba.

- Advertisement -

Neman shawara ba laifi bane amma yadda matan aure keyi a groups da dama a gaskiya bai kamata ba.

Sai ka ga matan aure ta fito social media group wai tana neman shawara kamar haka…

Dan Allah ina neman shawara “Mijinane ya shiga wanka sai naga budurwarshi ta yi masa sms wai ina zasu hadu” me zanyi?….. ko kuma ka ga “Dan Allah ina neman shawara Mijina ne yana neman aure bai fadamin ba sai naji a gari mai kuke gani zanyi… “Dan Allah shawaranku nake nema mijina sai yau yake fadamin za’a daura mishi aure ya zanyi…. Dan Allah ku bani shawara maman mijina ce ta sani gaba ko kaji mace ta ce yan’uwan mijinta da sauransu…..

Wanda yin hakan tona asirin gidan aurenki ne. A haka kuma wai ita nan kishin mijinta da kanta takeyi amma tana tona asirin gidan auren ta.

Abun haushi ma wai kaga harda yan’mata da basu yi aure ba ke bada shawara… Idan mai hankili ciki tayi comment na hankali sai kaji anmata caa da bakaken maganganu. Shin a hakane zaki hana mijiki neman mata kokuwa hakane zai sa dangin mijinki su so ki bayan baki da sirri.

Cikin group ko page din da kike posting kila ma budurwan mijin naki na ciki wani abunma sai kaga wasuma screenshot suke yi suna sakawa a status ko a tura wani group din a hakadai sirrinki ya game duniya har makusantanki da suka san labarinki a zahiri su gani harda dangin mijin naki ma. To dan Allah ribar me kika samu? Kuma shawaran da duk za’a baki bazai canza abunda Allah ya rubuta ba.

Kuma idan an duba cikin group din ko facebook page ne akwai baiwar da Allah yama kowa amma da wuya kaga ana cewa na iya kayan gyaran jiki zansa rana kuzo na koya maku, na iya girke girke zan koya maku kyauta na iya kayan kamshi na gida zan koya maku. Zan koya maku darasin littafi kaza na adddini ko na zamani.

Zai yi wuya kaji wata tace yau naje taro makarantan yarana naga anyi abunda ya burgeni ina so na fada muku domin kuma yaranku su karu zai yi wuya kaji haka haba!!! Mata…. ko kuma a samu wata rana ace za’ayi maganan tarbiyan yara ne wanda acikin group dinnan wasu basu iyaba wasu ko “Assignment” basu iya yiwa yaransu ba ma amma kullun suna nan neman shawara.

Wani lokuta sai dai kaga tallan magunguna na mata su kuma mata sai comment da neman farashi da location ko your contact shikenan.

Yar’uwa ko kinsha maganin mata idan har baki iyar tafiyar da rayuwan gidan aurenki ba toh da sauranki..

Dan Allah yan’uwa mata mu hada kai da hannu dan ganin mun gudu tare mun tsira tare mu nunawa juna hanyar kusanta ga Allah. Mu koya ma juna kai wa Allah kukan mu. Mai aure ki mika mijinki, auranki, zuri’arki da danginsa ga Allah kiriki ibada koda ma ana yi maki abunda baiyi daidaiba Allah yanaji kuma yana gani shine zai miki magani. Ki koyi yadda zaki magance matsalar gidanki ba tare da duniya ta saniba Yar’uwa.

Amma kina tona sirrin aurenki a media gobe kifito kina tunkaho yan group suna nunaki suna cewa dalla can sai kace ba itace ke neman shawara ba kwanaki wai mijinta yamata kaza da sauransu.. Dan Allah masu aure surika nunawa marasa aure mahimmancin aure da kuma cewa soyyar waje daban rayuwan zaman aure kuma bautan Allah ne. Zaurawa kuma su sani zawarci kaddaran sune su ma surika gyrawa wanda suke ciki da kuma nunawa yan’mata kura kuran da yakamata su sani domin gudun yawan mutuwar aure

Mata yakamata mu sani mune makaranta ta farko ga yayanmu Saboda haka mu gyara zamantakewarmu.

Nagode daga yar’uwar ku Sulaiman Hauwau Lere

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: