Ku daina wadannan halaye 2 domin kamaceceniya da Iblis ne

An ruwaito cewa wata rana wani mutum ya ce ma Shaidan (Iblis) “Ya Aba Murrata!, ya zan yi in zamar kamar kai wajen sa6o?”

Sai Iblis ya ce masa “Kaiconka!, ba wanda ya ta6a nemar wannan bukata a wajena saikai. Me yasa kake son zama kamar ni?”.

Sai mutumin ya ce “Ni dai kawai ina so ne”.

Sai Shaidan ya ce “To indai kana so ka zama kamar ni wajen sa6o, to na farko ka wulaqanta Sallah na biyu kuma ka dinga yawan rantsuwa ko kana da gaskiya ko baka da gaskiya”.

- Advertisement -

Da jin haka sai mutumin ya ce

“To ni kuma na yi wa Allah alqawari cewa ba zan ta6a wulaqanta Sallah ba kuma ba zan ta6a yin rantsuwa ba ko ina da gaskiya ko ba ni da gaskiya”.

Da Shaidan ya ji haka sai takaici ya kama shi. Ya ce

“Wallahi ba wani mtum da ya ta6a samun nasiha a wajena ta hanyar yaudara saikai amma na yi alqawarin ba zan sake yiwa wani DanAdam nasiha ba”

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: