Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKu tashi mu farka yan Arewa, yaki zai cimu muna barci

Ku tashi mu farka yan Arewa, yaki zai cimu muna barci

 

Daga Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.

Daya daga cikin arzikin da Allah yayi wa Arewa shine yawan al’umma, tun kafin zuwan turawa yankin Arewa ya fi yankin kuduncin kasar nan yawan al’umma kuma daya daga cikin ribar yawan al’ummar Arewa shine yawan masu jefa kuri’a lokacin zabe, wanda hakan ta sa duk wata jam’iya ko kuma dan takara yake neman goyon bayan Arewa a lokacin zabe musamman na shugabancin kasar nan, domin wuka da nama na hannun dan Arewa, idan aka zo maganar wa zai ci zabe.

Amma sai ga shi muna nema mu bari wannan dama ta wuce mu, a aikin yin sabuwar rinistar zabe da ake yi yanzu na online wato na yanar gizo gizo kafin a kai ga yin na gari yadda aka saba a mazabu.

- Advertisement -

Tun sanda hukumar zabe wato INEC ta fara yin wanan aikin rijistar katin zabe na online wata daya da ya wuce zuwa yanzu, wanda na sababbin masu yin zabe ake, kawo yanzu mutane fiye da 800,000 ne suka yi rijistar, kuma a cikin wannan lambar gaba daya jihohin Arewa sha tara, kimanin mutane 130,000 su kai rijistar, daga cikin wannan kuma jihohin Kogi da Kwara kadai su suke da kusan 50,000 inda sauran jihohi sha bakwai suke da 80,000, a Kano kasa da mutum 13,000 ne kawai su kai rijista, gaskiya wannan da kunya.
Idan akai la’akari da jihohin Kudu guda sha bakwai, suna da mutane da su kai rijista kimamin 670,000, kuma a cikin su, karamar jihar Osun kadai mutane fiye da 250,000 suka yi rijista kawo yanzu (ita kadai ta fi yawan jihohin arewa gaba daya har ta kusa ninka wa sau biyu ma) Lagos da Edo da Bayelsa da Anambra kowacce tana da kimanen 50,000.

Ina kira da masu ruwa da tsaki a Arewa da su kara wayar wa da al’ummar Arewa kai akan wannan aikin rijistar saboda muhimmancin sa, ko baza kai zabe ba, katin zabe na da muhimmanci domin akwai shirye shirye kala kala da gwamnatoci ke bujuro da su wanda za’a ce sai mai katin zabe ne kadai zai mora. Idan baka iya yi ba kai da kan ka, ka samu wanda zai maka, ko ka je cafe ai maka. Ba shi da wahala kuma ba bata lokaci.

Latsa wannan link din domin ya kai ka shafin da za kai rijistar cikin sauki.
https://cvr.inecnigeria.org/Home/start

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: