Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKuskuren da ake yi wajen tsarki dake jawo babbar matsala ga lafiyar...

Kuskuren da ake yi wajen tsarki dake jawo babbar matsala ga lafiyar iyali

Kuskuren da ake yi wajen tsarki dake jawo babbar matsala ga lafiyar iyali

Daga Aisha Aliyu Shanono

Yau zamu tattauna akan tsarki domin da yawan iyaye Mata suna kurskure wajan yima yara tsarki da su kansu iyayen. Wannan kurskuran yana jawo mana matsaloli a rayuwar mu ta yau da kullum.

Anayin tsarki daga dukan abinda ya fito ta daya daga cikin mafita biyu gasu kamar haka:-

- Advertisement -

1.Tsarkin fitsari
2.Tsarkin bayan gida

Zamu fara da tsarki fitsari
Uwar gida kina bukatan ruwa mai tsafta kuma mai dumin domin jiki mace kwata kwata baya bukatan ruwan sanyi don haka ruwan dumi kike bukata. Zaki fara wanke hannuwanki sannan ki dauko wannan ruwan dumin ki wanko mata gabanta, iya gaban kawai ake da bukanta hannun ki ya wanko ki wanke da kyau uwargida kada ki kuskura ki saka mata sabulu a gaban ta domin sabulu na kawo cancer gaba. Ki kuma tabattar ta gaba kika wanke,
Domin wasu iyayan ta baya suke tsarki wanda yake wajo matsaloli da dama.

Tsarkin bayangida: Uwargida ki bani aran hankalin ki da kyau domin babbar matsalar anan take, tsarkin bayangida ba lalle sai da ruwan dumi ba anma kina bukarta ruwa me tsafta, mu daina barin yaran mu na goye suyi bayan gida kuma kunzugun su (diapas) din ya dade musu ko kuma mu barsu akan fo su dade domin matsalolin da hakan ke haifarwa ga lafiyarsu. Wannan bahayan kwata kwata ba’a so ruwan shi ma ya taba gaban mace balle kuma ace mu barshi ya dade a jikin su.

Ga kadan daga cikin illolin da yin hakan ke jawowa:-

A. Wannan warin yana koma wa gaban mace wanda yake hadasa mata warin gaba.

B. Yana kawo cututtukan gaba wato Infection

C. Daukewar sha’awa

D.Daukewar ni’iman gaban mace

E. Yana jawo matsaloli ga ma’aurata su rasa ta ina matsalan take ashe tun farko uwargida ke kika jawowa yarki wannan matsala maganin kada ayi kada a fara.

A wannan gabar zan tunasar da Uwar gida da me gida cewa wannan aiki fa duka namu ne, uwargida ke ce me yi kai kuma me gida naka saka ido ka tabbatar ana yin yadda ya dace kodayake kaima kana iya saka hannu kayi kai da kanka.

Uwargida ki tabattar kin cire mata wannan kunzugun tana yin bayan gida ki tsugunar da ita da kyau ki fara da wanke mata gabanta da kyau da kuma ruwa mai tsarki, ki tabattar kin wanke gaban nan sosai da ruwan dumi saiki koma ta bayan ta ki wanke bayan gidan sosai zaki iya saka sabulu ki wanke bayan karki bari wannan ruwan ya taba mata gaban ta balle kuma ki sako hannun ki, ki ce zaki wanke gaban kuma wato cakudede niya kenan a’a sai kin tabattar kin gama da gaban sannan sai ki koma bayan ba’a so ana hada su waje daya domin gaban mace tamkar jariri yake wajan daukan cututuka..

Uwargida ki saka ma yarki ido wajan ganin yadda take tsarki domin wasu kawai daga baya suke farawa maimakon a fara da gaba sai a koma baya daga lokacin da yarki ta kai shekara goma ki haramta mata amfani da ruwan sanyi sai ruwan dumi domin hakan ba karamin illa yake jawo ma rayuwar ta ba, har shima mai gida ba’a so ya dinga yawa amfanin da ruwan sanyi ki kula da kyau Yaruwa. Wasu suna ganin kamar iyaye ne kadai ke da bukatar yin amfani da ruwan dumi a’a karamin kurskure ke haifar da babban matsala, su ma ‘yayan mu suna bukata. Tare da fatan uwargida da mai gida mun karu!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: