Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBudurwar da Saudiyya ta jefa kurkuku bisa zargin kwayoyi ta zama jami'ar...

Budurwar da Saudiyya ta jefa kurkuku bisa zargin kwayoyi ta zama jami’ar NDLEA a Nigeria

Daga Muryoyi

Yar Nigeria daga jihar Jigawa, Zainab Aliyu Kila wacce kasar Saudiyya ta daure tsawon kwanaki 124 bisa zargin samun miyagun kwayoyi a cikin kayanta lokacinda taje aikin Hajji tare da iyayen ta a 2018 ta zama jami’ar NDLEA

Muryoyi ta ruwaito daga majiya mai tushe Zainab Aliyu na cikin mutane 2,000 da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA dake Jos a jihar Plateau ta yaye a jiya Juma’a

A ranar 26 ga watan Disamba, 2018 ne Kasar Saudiyya ta kama Zainab bisa samun miyagun kwayoyi na tramadol a cikin kayan ta bayan ta sauka filin jirgin Jeddah daga filin jiragen Mallam Aminu Kano tare da mahaifiyarta Maryam, da kanwar ta, Hajara.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito bayan hukumomi a Nigeria da Saudiyya sun tsananta bincike sai suka gano ashe wasu ne suka makala sunan ta a jikin wata jakar miyagun kwayoyin. Bayan an gano bata da hannu a ciki sai aka sake ta a ranar 30 ga watan Afrelu, 2019 sannan aka maido ta Nigeria bayan makwanni Biyu.

Mahaifin budurwar, Habibu Kila, ya tabbatar wa da majiyarmu cewa diyarsa ta zama jami’ar NDLEA kuma ta fita a matsyin “Assistant Narcotic Officer”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: