Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMafi yawan Almajirai dake gararamba a tituna ba yan Nigeria bane –inji...

Mafi yawan Almajirai dake gararamba a tituna ba yan Nigeria bane –inji Ganduje

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce mafi yawan Almajirai gararamba a titunan Nigeria ba yan Nigeria bane bakin haure ne daga kasashen Nijar, da Chadi da kuma Cameroun

Ganduje wanda ke jawabi a wajen bikin bude wata bitar kwanaki Uku kan ilimi da ya gudana a ranar Litinin ya ce shi yasa aka kasa shawo kan matsalar almajiranci a kasar, domin da zaran ka inganta fannin almajiranci sai su kara kwararowa cikin kasar.

Yace shi yasa yanzu Gwamnoni suka dukufa kokarin ganin an saka wata doka da zata dakile yawaitar kwararowar bakin haure a tsakanin jihohin kasarnan

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito tuni Gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu a kan wata doka da ta tanadi hukuncin dauri a gidan yari ko kuma cin tara ga duk iyayen da aka samu da laifin ƙin sanya ƴaƴansu a makarantar boko a jihar.

Domar ta ce ya zama wajibi iyaye su sanya yaransu da suka isa zuwa makaranta a makarantu.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: