Daga Muryoyi
Akalla maguzawa 314 ne suka karbi addinin musulunci a garin Gidan Goje dake karamar hukumar Takai a yau Litinin,
Maguzawan sun shaidawa majiyar Muryoyi cewa; Ra’ayin kan su ne suka musulunta ba don an tilasta su ba ko kuma don ko wai za’a basu wani abu ba.
Muryoyi ta ruwaito maguzawan sun musulunta ne a hannun shugaban kungiyar Izala na kasa Abdullahi Bala Lau, da Gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da shugaban darikar Kadiriyya Sheikh Kariballah Nasiru Kabara, da Sauran manyan malamai daga kungiyoyi daban-daban,
- Advertisement -
Ganduje wanda ke jawabi a madadin gidauniyarsa ta Ganduje Foundation yayi alkawarin za su gina masu babban masallacin Juma’a da makaranta domin ilimantarwa da kara dabbaka addinin Musulunci a Garin na Goje.
Daga bisani an rabawa sabbin musuluntar tufafi, kayan sawa da sauran abubuwan bukata.