Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMajalisa bata da hurumin gayyatar Buhari kan sha’anin tsaro –inji Malami

Majalisa bata da hurumin gayyatar Buhari kan sha’anin tsaro –inji Malami

Daga Muryoyi

Antoni Janara na kasa kana Ministan Shara’a, Abubakar Malami a yau Laraba ya ce majalisar dokoki ta tarayya ba ta da hurumin umurtar Shugaba Muhammadu Buhari ya gurfana a gabanta don ya yi mata bayani kan sha’anin tsaro,

Ministan ya ce sha’anin tsaro sirri ne wanda doka ta baiwa ofishin shugaban kasa cikakken iko akai sai yadda ya so zai yi doka ta bashi dama.

Don haka a cewar Malami bai zama wajibi Majo Janaral Muhammadu Buhari ya amsa gayyata ko ya je gaban majalisar ba. Idan kuma ya je to wannan ra’ayinsa ne amma ba wai don tilascin da majalisar tayi masa bane.

- Advertisement -

A gobe Alhamis ne dai ake sa ran Manjo Janar Buhari zai gurfana a gaban zauren majalisar dokoki da sanatoci domin amsa tuhume-tuhume kan gazawar Gwamnatinsa a fannin tsaron ratuyuka da dukiyoyin yan Nigeria

Sai dai a cewar Ministan shara’ar, Shugaba Buhari ya kawo gagaruman sauyi da cigaba a fannin tsaron kasarnan wanda ya zama wajibi a yaba masa.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: