Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMaryam Yahaya ta koma ga Allah a shafinta

Maryam Yahaya ta koma ga Allah a shafinta

Daga Muryoyi

A yan kwanakin nan ne dai labarin rashin lafiyar jarumar fina-finai Maryam Yahaya ya karade kafafen sadarwa inda kowa ke hasashen cutar dake damun jarumar sai dai mafi yawan ana zargin jifar jarumar akayi wato asiri.

Muryoyi ta ziyarci shafin jarumar a Instagram (real_maryamyahaya) da yammacin ranar Litinin inda tayi kicibis da hoton daki mai tsarki Ka’abah da Al-Kurani sannan akayi rubutu cikin larabci mai dauke da addu’ar neman tsari wato “bismillahillazi la yadurru ma’asmihi syaiun fil ardi wala fissamai wahuwas sami’ul ‘alim” alamun dai jarumar ta saduda ta fawwalawa Allah al’amuran ta.

Mutane da dama sun yaba tare da yi mata addu’ar Allah ya bata lafiya.

- Advertisement -

Mutane da dama na da bambancin ra’ayi game da harkar fim a yayinda wasu ke sukar jaruman wasu kuma na yaba masu, jarumar dai ba kasafai take wallafa abubuwan addini a shafukanta ba hasalima hotunan ta ne suka cika birjik amma sai gashi ta wallafa abu mai alaka da addini wanda hakan wasu ke ganin tamkar ta saduda ne ta koma ga Allah gadan-gadan. Muna taya ta addu’ar Allah ya bata lafiya

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: