Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMatar dake kai makamai Kaduna, Zamfara, Katsina, Sokoto, Niger da Kebbi ta...

Matar dake kai makamai Kaduna, Zamfara, Katsina, Sokoto, Niger da Kebbi ta shiga hannu

Daga Muryoyi

Rundunar yan sanda a Zamfara ta kama wata mata Fatima Lawali wacce ta kware wajen yin safarar makamai ga yan bindigar dake addabar jihohin Zamfara, da Sokoto, da Kebbi, da Kaduna, da Katsina da kuma Niger.

An kama Fatima ne a kauyen Gada Biyu dake cikin karamar hukumar Bungudu da abarusai na AK-47 har kusan guda duba Daya.

A cewar matar, ta yi safarar makaman ne daga Kauyen Dabagi dake jihar Sokoto zata kaiwa wani kasurgumin dan bindiga dake kai hare-hare a yankin Zamfara da makoftan jihohi, Ado Aliero.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito rundunar yan sandan har wayau ta kama wani mutum Babuga Abubakar dake kauyen Mayana a Gusau ta jihar Zamfara dake hada baki da yan bindiga.

Rundunar yan sandan tace ta kama shi ne a Gusau biyo bayan wasu bayanan sirri da ta samu akansa. Binciken sirri ya tabbatar da Babuga yana hada kai da gungun yan bindiga irinsu Lawali Na’eka dake addabar Maradun da Almeriya dake addabar Bungudu.

A cikin bayanan sa Babuga Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa sune suka hadu su kusan 100 suka kai hari a kauyen Wanke dake Gusau babban birnin jihar Zamfara inda suka yi barna kana sukayi awon gaba da shanu fiye da 240 na jama’a.

Kwamishinan yan sanda reshen jiharZamfara Ayuba Elkanah ya ce suna cigaba da binciken yan ta’addan kafin su gurfanar dasu a gaban shara’a.

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: