Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMatasa 11 sun mutu a hanyar zuwa jarabawar shiga aikin soja a...

Matasa 11 sun mutu a hanyar zuwa jarabawar shiga aikin soja a Kano

Mutum 11 sun mutu a wani hadarin mota da ya rutsa dasu a hanyar Kano zuwa Jigawa, matasan na tafe ne zasu je Kano daga kauyen Gagarawa domin jarabawar shiga aikin Sojan sama

Muryoyi ta ruwaito kakakin yan sanda na jihar Jigawa, Audu Jinjiri, ya ce hadarin ya auku ne a lokacinda motar da matasan ke ciki wata Golf 3 wagon, ta afka karkashin wata babbar motar DAF dake tsaye a titin ta lalace

Wadanda hadarin ya rutsa dasu sun hada da, Auwalu Mohammed (Dreban motar tasu); Mutari Sule; Ibrahim Sani; Katimu Muhammad; Dauda Salisu; Musbahu Yakubu, Rabiu Muhammad-Ado; Salim Muhammad-sani; Akibu Ubali-sale; da Murtala Salisu, da kuma wani cikinsu da ya rasu a asibiti

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Kakakin yansandan na cewa tuni sun kama dreban babbar motar Aminu Hassan, domin.

Matasan sun bar gida tun wajajen karfe 5 na asubahin ranar Asabar da nufin su isa Kano da wuri domin su samu su yi jarabawar shiga sojan

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: