Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMatashi a Bauchi ya kashe yaro ya cire idanunsa don yin kudi

Matashi a Bauchi ya kashe yaro ya cire idanunsa don yin kudi

Daga Muryoyi

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi Musa Hamza, dan shekara 22, bisa zarginsa da kashe wani yaro Adamu Ibrahim sannan ya cire masa idanuwa sai ya kona gawarsa ya bizne a Unguwar Wake dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi.

Muryoyi ta ruwaito kakaki yan sandan Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce matashin ya amsa laifinsa kuma lamarin ya faru ne a ranar 21/12/2020.

Ya ce wanda ake zargin bayan ya kashe yaron ya kona gawar sai kuma ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa sannan ya bizne kowane sashin jikin a waje daban-daban.

- Advertisement -

Matashin ya amsa laifinsa kuma ya ce bokan sa ne ya saka shi aikata wannan ta’addaci domin yana so yayi kudi

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: