Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMatashin mawaki daga Bauchi ya mutu a hanyar zuwa inda aka tura...

Matashin mawaki daga Bauchi ya mutu a hanyar zuwa inda aka tura shi bautar kasa

Daga Muryoyi

Mummunan hatsarin mota ya ritsa da wani matashi dan bautar kasa mai shekaru 24 dan asalin jihar Bauchi, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa jahar Katsina domin halartar horaswa na sati uku.

Majiyarmu Muryoyi ta rawaito hatsarin ya faru ne a ranar Juma’a da rana a jahar Jigawa akan hanyarsa ta zuwa sansanin yan bautar kasa dake jihar Katsina, Kazalika wani mutum daya shima ya rasa ransa a hatsarin.

Mamacin wanda ya soma fice a fagen waka ya fito ne daga Ungwan Maryam a karamar hukumar Tafawa balewa dake jahar Bauchi kuma bayanai sun nuna shine na farko acikin yan’uwansa su hudu da ya kammala karatunsa a makarantar kimiyya da fasaha ta kasa dake jahar Bauchi a inda yayi karamar duploma da babbar dupuloma

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: