Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMuhimmancin kunya ga diya mace

Muhimmancin kunya ga diya mace

Daga Fatima S. Abdul

Hausawa suna cewa kunya adon mata, mace mai kunya misalin gishirine a cikin miya, ita ce adon al’umma, kuma itace hasken dake haskaka al’umma, domin kuwa mace ta shafi kowane bangare na al’umma,

SHIN MECECE KUNYA

Kunya wata dabi’a ce da take hana mutum aikata duk wàni abu mara kyau ko mummunan ai Wanda ka iya zubarwa mutum da girnansa, kimarsa, da mutuncinsa a idon mutane. Sannan tana jagorantan mutum zuwa ga aikata kyakkyawan aiki Wanda zai daga darajarsa à idon mutane….

- Advertisement -

duba ga ma’anar kunya da nayi bayani a baya zamu gane cewa kunya abuce mai kyau ga

NAMIJI, MACE, YARO, YARINYA, TSOHO, DA TSOHUWA ….sai dai anfi bukatar ta ga mace domin kuwa rashin ta ga ya mace babbar illace kuma barazana ne ba a gareta ba ita kadai ga al’umma baki daya, domin idan mace daya ta gyaru tamkar al’umma ce baki daya ta gyaru haka zalika idan ta baci al’umma ta baci….

Da yawan mata a yanxu sun watsar da dabi’ar kunya a rayuwarsu inda suka dauko rashin kunya suka sa ma Kansu duk da sunan wayewa, duba da yadda mutane yanxu suke daukan mace mai kunya à matsayin wacce bata waye ba, mace Mara kunya kuma itace wayayyiya, wannan wai shine cigaba ‘cigaban mai haqan rijiya kenan’

Misalin mace mai kunya da Mara kunya, misalin alewa ne budaddiya da rufaffiya…

Mace mai kunya al’kyabbar mata
Mace mai kunya jarumar mata
Mace mai kunya jarice
Mace mai kunya sinadarin gida
Mace mai kunya fitila ce
Mace mai kunya ado ce
Mace mai kunya jagorace
Mace mai kunya wajen magana da aiki Alkhairice

Kunya dabi’a ce mai kyau a addinance da al’aladance, haka kuma babu addinin da ya goyi bayan rashin kunya, sannan tana da muhimmanci ga dukkan al’umma, duk abinda àkace yana da muhimmanci barinsa babu shakka illace ga mutane baki daya

Yake yar’uwata mace ki zama mai kunya, domin daga darajarki, kimarki da kuma martabar ki ta ya mace, domin ke din fitilace ga Al’umma kuma abin koyi ce, kunya kuma adoce a gare ki….

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: