Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMuhimmiyar shawara ga masu fuskantar tsana a wajen aiki

Muhimmiyar shawara ga masu fuskantar tsana a wajen aiki

Daga Muryoyi

Wani abokina da mukayi yarinta tare wanda yanzu yake aiki a banki ya taba gayyata ta wajen taron sunan matarsa, amma bayan mun je wajen sai na lura mafi yawan kujerun da aka kebe domin abokansa na wajen aiki wayam babu kowa da ya zo.

Hakanan ma a bangaren sauran abokansa na wajen da yake zuwa ibada duk babu kowa, indai takaice maku gaba daya kashi 20% na bakin da aka gayyata suka halarci wannan taro dakin taron babu kowa ga kujeru nan birjik amma ba kowa akansu. Allah yaso naje da iyali na da wasu daga cikin abokai na shine ma na samu suka dan zazzauna a wajen dakin taron ya dan cika yayi kyawun gani.

Abun ya dame ni matuka har na kasa hakuri bayan taron na sami matarsa nake tambayar ta ko bai gayyaci abokan aikinsa bane don naga ba wanda ya zo? Sai kuwa ta kada baki tace dani “Ya gaya masu, amma da gangan suka ki don dama gaskiya yan ofis din nasu sun tsane shi saboda shine akanta mai binciken kudade a wajen aikin nasu”  ta cigaba da fada mini cewa “Har muma iyalansa bamu tsira ba domin ba a jima ba wata a ofis dinsu ta kirawo ni a waya tana ta yi mani barazana ga rayuwa ta wai saboda mijina ya bincike ta kan wata badakala da aka zarge ta a ofis kuma ya same ta da laifin da ake zarginta saboda haka a lokacin ya bayar da shawara a kore ta daga aiki”, haka dai nayi zugum tana ta bani labari.

- Advertisement -

Bayan na dawo gida abun ya tsaya mini a rai ina ta tunani ya zanyi inda nine shi? Shin irin haka na faruwa a rayuwar ku? Mecece mafita?

EDITAN MURYOYI: Aiki na iya zama tushen rashin farin ciki don mutane da yawa kuma saboda dalilai da yawa. Ba tare da wata shakka ba, aiki abu ne mai mahimmanci, tunda yana samar mana da abin da zamu rayu, sai dai kuma kash wani abu kuma da zai iya bamu matukar bakin ciki a wajen aiki shine mummunan yanayi tare da abokan aiki. Saboda dalilai daban-daban yana iya kasancewa abokan aiki ba sa jituwa wanda hakan ke haifar da mummunan yanayi har ma muji aikin ya fita mana a rai.

Da farko dai ina so kasan cewa babu yadda za ayi duk duniyar nan kowa ya hadu yaso ka ko a hadu a ki ka, koda kuwa kai akanta ne kai ko ma wace irin sana’a kake yi. Wasu zasu so ka wasu zasu ki ka. Rayuwa ta gaji haka.

Sai dai yana da kyau a duk aiki ko sana’ar da mutum yake yi, to ya rika duba mu’amalarsa, ya tabbatar yana da mu’amala mai kyau. Ya rike gaskiya sannan yayi aiki da kwarewa komi kankantar aikin.

A daya bangaren kuma dama ita gaskiya daci gareta, a duk sanda mutum ya rike gaskiya to fa ya shirya fuskantar kalubale iri-iri musamman a waje irin wanda ya jibanci bincike ko ladaftarwa. Domin a irin wannan wajen zaka iske zabi biyu kake dashi ko dai ka fallasa wata rashin gaskiya ko barna ko kuma ka boye raahin gaskiyar ko barnar kana ji kana gani. Wanda yin hakan ba daidai bane.

Wannan kuma shi yafi yawa a halin da muke ciki a yau, zaka ga indai mutum yace zai yi abunda ya dace a waje to lallai sai dai Allah ya kyauta, domin sai mararsa gaskiya sun tsane shi sun yake shi a fili da boye kai a wasu lokutan ma har rasa rai ake yi!

Ina fata dai matar abokin naka ta kai rahoton barazanar kisan da akayi mata domin irin wannan abun ba a daukarsa da wasa…

Zamu duba ra’ayoyin ku akan wannan batu, me ke jawo a tsani mutum a wajen aiki? Me ya kamata wannan mutum ace yayi?…

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: