Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMuna taya duniyarmu ta rubutu murna bisa zuwan sabuwar Jaridar MURYOYI

Muna taya duniyarmu ta rubutu murna bisa zuwan sabuwar Jaridar MURYOYI

Muna farincikin gabatar maku da sabuwar Jaridar MURYOYI wadda aka fara bugawa da nufin bawa fannin yada labaru da aikin jarida sabon salo. Muryoyi na matsayin wata kafa ko murya ga kowa da kowa.

Kamfanin Manuniya Multimedia ne ke wallafa wannan kafar yada labarai. Muryoyi.com kafar yada labarai ce da aka kafa ta domin bai wa jama’a damar tofa albarkacin bakinsu da tattaunawa akan batutuwan dake da tasiri ga rayuwarsu da kuma zaburar da hukumomi sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na jama’a da cigaban kasa ba kage ba cin mutunci.

Manufar Muryoyi yada bayanai da rahotanni ingantattu da suka shafi addini, adabi, al’adu, siyasa, fasaha, zamantakewa, tattalin arziki da sauransu da nufin bayar da gudummuwa wajen bunkasa demokaradiya, habaka tattalin arziki, da kyautata jin dadin rayuwar al’umma.

MANUFA: Muryoyi ta kasance wata kafar yada labarai da bayanai masu inganci da ake iya dogara a kansu.

- Advertisement -

Sannan mu zama wata kafa da zata zama wajen gabatar da muhawara da tattaunawa akan batutuwan dake da tasiri ga rayuwar jama’a da cigaban kasarmu

BURINMU: Zamewa wata babbar kafar yada labarai a duniya da zata samu amincewar jama’a

Kafar yada labaran dai za ta canza taswirar yaɗa labaru a cikin Nigeria kuma tana zama muryar ga yan ƙasar da ma wadanda ba yan Nigeria ba, shuwagabannin da talakawan da ake shugaban ta, mata da maza, kowane addini ko kabila, mai lafiya ko marar lafiya.

Tun wasu shekaru da dama da suka wuce muke da wannan ra´ayi, wato samar da wata kafar yaɗa labaru da za ta zama akasin abubuwan da aka saba ji daga mafi yawancin kafofin yaɗa labaru.

Ana wallafa wannan kafar yada labarai ne a cikin harshen Hausa a duniyar yanar gizo wato intanet a www.muryoyi.com domin ta kai ga jama’a da yawa cikin sauƙi musamman masu iya sarrafa yaren Hausa. Baya ga rahotanni masu ƙayatarwa dake ƙarin haske akan batutuwan da suka shafi al´adu ana ƙawata kafar da hotuna masu ban sha´awa waɗanda ke ɗaukar hankalin mai karatu.

Muna nan a duka dandalin sadarwa a @Muryoyi

Mun dace da zabin ku!!!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: