Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuNa zabi Hajiya Asiya Balaraba Ganduje a matsayin gwarzuwata ta 2020 a...

Na zabi Hajiya Asiya Balaraba Ganduje a matsayin gwarzuwata ta 2020 a cikin mata

DAGA Bashir Abdullahi El-Bash

-A Karo Na Biyu Na Zaɓi Ƴar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, (Fulanin Zanna Laisu Fika) A Matsayin Gwarzuwata Ta Shekarar 2020 Duba Da Nagartarta Da Sadaukarwarta Wajen Gina Rayuwar Al’umma Musamman Matasa.

Yau Litinin, 4 Ga Watan Janairu, 2020.
A duk lokacin da jama’a su ka ji an kira sunan ƴar mai girma gwamnan Jihar Kano, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje (Fulanin Zannan Laisu Fika), babban abin da ya ke zuwa cikin tunaninsu shi ne nagartarta da alkhairanta, da haba-habarta da jama’a, da tausayinta da jin ƙanta ga al’umma.

Ta fuskar mu’amala da jama’a, Fulanin Zanna ta sha bamban da sauran ƴaƴan manyan mutane a Nageriya, domin kuwa maca ce wacce ta ke da ɗabi’ar girmama al’umma. Duk ƙanƙantar matsayin mutum a cikin al’umma ba ta raina shi, ta na karɓar al’umma ta yi haba-haba da su ta ƙanƙan da kai ta saurari matsaloli da buƙatansu ta kuma magance musu damuwar da su ka je mata da ita gwargwadon iko.

- Advertisement -

Hajiya Asiya Balaraba Ganduje, mace ce wacce ta ke da matuƙar haƙuri da kawaici gami da yafiya ga duk wanda ya ɓata mata. Irin ɗabi’u da kyawawan halayen manzon Allah (S.A.W).

Idan mu ka yi duba halayenta na kishin addininta na Islama, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, mata ce wacce Allah ya azurta da zuciyar ƙaunar addininta na musulunci matuƙa. Domin kamar yadda mahaifinta ya ke musuluntar da maguzawa, ita ma ta siffantu da wannan ɗabi’a kuma a duk Nageriya babu wata ƴar gwamna da ta ke musuluntar da Maguzawa sai ita. “Ƴar Aljannah”, kamar yadda jama’a su ke yi mata fata saboda nagarta da kyawawan halayenta na taimakon addini da jin ƙan al’umma.

Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta tallafawa ɗumbin jama’a da kuɗaɗen yin jari da tallafin karatu ga ɗalibai a cikin gida Nageriya da kuma ƙasashen waje. Ta tallafawa marayu da gajiyayyu waɗanda ba za su taɓa lissafuwa ba saboda yawansu. Ta gina al’umma ta samar musu da ayyukan yi a cikin gwamnati da harkokin kasuwanci da sana’a. “Uwar Marayu gatan marasa gata har ma da masu gatan”. Kamar yadda jama’a su ke yi mata kirari saboda karamcinta.

Ko da a ƙarshen shekarar 2020, Fulanin Zanna ta kashe zunzurutun kuɗi sama da Naira Miliyan (20) wajen ɗaukar nauyin karatun ɗumbin matasa ƴaƴan talakawa da kuma tallafawa wasu, waɗanda yawansu ya kai sama da matasa (300) a sassa daban-daban na wannan Jiha da ma Arewacin Nageriya gaba ɗaya.

A saboda irin wannan ɗumbin ayyukan alkhairai da ta ke yi a ciki da wajen Jihar Kano, Hajiya Asiya Balaraba, ta samu laƙabin suna (Garkuwar Matasan Arewa) domin ba wai a Jihar Kano kaɗai alkhairanta ya tsaya ba, mata ce wacce ta zama hantsi mai leƙa gidan kowa a Arewacin Nageriya. Ba ma Arewa da Nageriya ba, har a Nahiyar Afrika gaba ɗaya Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta samu lambar yabo daga ƙungiyar mawaƙa da masu sana’ar shirya Fina-Finai na Afrika.

A cikin gida Nageriya kuwa, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta samu lambar yabo daga wurin aikinta, kamfanin mai na ƙasa (NNPC) inda su ka karrama ta da babbar lambar yabo sakamakaon ƙwazo da himmarta. Baya da haka, ta samu lambobin yabo daga ƙungiyoyi daban-daban na malamai da ɗalibai na makarantun boko da na islamiyya, a ƙoƙarinsu na yaba mata kan tallafi da gudunmawar da ta ke bayarwa wajen cigaban harkokin ilimi da al’umma.

A fannin gudunmawar da ta ke bayarwa a wajen taimakawa mahaifinta da gwamnatinsa kuwa, har laƙabi al’umma su ke yi mata da (Garkuwar Gwamnatin Baba Ganduje), duba da yadda ta zamto tsaro da kariya daga hare-haren maƙiya da ƴan adawa. Ɗumbin al’umma ne yau su ke tare da Baba Ganduje da gwamnatinsa a sanadiyyarta.

Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje ta kasance mata wacce ta shiga loko da saƙo ta tallafawa al’umma masoya da maƙiyan Baba Ganduje da gwamnatinsa ta yadda a sanadiyyar hakan maƙiyan sun zama masoya, masoyan kuma su ke cigaba da ƙara ƙarfafa ƙauna da soyayyar da su ke nunawa.

Yau a Nageriya, Babu wata ƴar gwamnan ada ko a yanzu da aka taɓa ganin ta na ƙoƙari da taimakawa mahaifinta da gwamnatinsa da ƙara masa yawan masoya da magoya baya kamar Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje. Ita kaɗai ce ba a yi ba kuma babu kamarta.

Fulanin Zanna, kuɗinta ta ke fitarwa ta kashe akan neman cigaban mahaifinta da gwamnatinsa sannan kuma ita da kanta ta ke shiga loko da saƙo a zaɓukan da su ka gabata domin nemawa mahaifinta goyon bayan al’umma, kuma da wannan taimako nata an samu gagarumar nasarar da ƙila da ba ta ba da gudunmawa, sai an fuskanci matsala da ba za ta gyaru ba.

Yau a sanadiyyar Hajiya Balaraba, ɗumbin talakawa masu yin zaɓe su na biyayya da Baba Ganduje. Ɗumbin mawaƙa da masu shirya fina-finai da marubuta da ƴan jaridu da ƴan midiya duk su na tare da Baba Ganduje a sanadiyyar ɗumbin alkhairan Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje da ya same su.

Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta kasance mata wacce ba ta ƙin amsa gayyatar duk wani taro da aka gayyace ta ko da kuwa taron na talakawa ne. Ba kamar wasu ƴaƴan manya ba waɗanda in ka ga sun je wani taro ko biki to ya shafi abokansu ne ko ƴan uwansu ƴaƴan manya. kuma ko da ba ta samu damar zuwa da kanta ba to ta na tura wakilci domin ganin ta mutunta wannan gayyata da aka yi mata.

Haka zalika dukkan wani taro da ake buƙatar gudunmawarta domin a gudanar da wani abu da zai kawo cigaban addinin musulunci da al’umma gaba ɗaya, Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta na ƙoƙari ta ga ta bayar da gagarumar gudunmawa ko da ba ta je da kanta ba.

Kamar yadda ta saba a duk shekara ko da a watan Ramadan na shekarar 2020, (Tauraruwar Matan Arewa), ƴar mai girma gwamna, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta tallafawa dubban talakawa mabuƙata da tallafin kuɗaɗe da kayan masarufu waɗanda su ka haɗa da shinkafa da taliya da suga da sauran abubuwan buƙata na rayuwa na ɗan adam domin gudanar da ibadar azumi cikin nutsuwa da walwala.

Sakamakon annobar (Covid-19) da aka fuskanta a wannan shekara, Fulanin Zanna ta ninka ayyukan jinƙan nata ya ƙara shafar ɗumbin al’umma da dama sannan kuma ta fara da wuri tun ma kafin lokacin azumin.

Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta ba da gudunmawar zunzurutun kuɗi har Naira (200,000) domin a gyarawa wata mata gidanta kamar yadda Marubiciyar nan mai ƙoƙarin nemawa jama’a taimako, Malam Fauziyya D. Suleman, ta sanar a shafinta na sadarwar zamani.

Wannan shi ne ya ke ƙara shaidawa duniya yadda Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta ke ƙoƙari matuƙa wajen ganin ta taimaki rayuwar al’umma a birane da karkara na Jihar Kano har ma da sauran Jihohi.

A saboda ayyukanta na alkhairi da kuma yadda ta ke da muhimmanci da daraja a idanun al’umma, Jama’a ne su ke yi wa Hajiya Asiya Balaraba Ganduje laƙabi da sunaye masu daraja waɗanda su ka haɗa da, “ƴar Aljannah, Tauraruwar Matan Arewa, Garkuwar Matasan Arewa, Uwar Marayu, Gatan Marasa Gata har ma da masu Gatan, sarauniyar al’umma”, Gamji Sha Sassaƙa, kowa ya ga zabuwa da zane nta ya ganta”.

Babu ko shakka Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ta kasance tauraruwa wacce ke haske a ciki da wajen Jihar Kano. Kuma a kullum farin jininta da girmanta ƙara ƙaruwa ya ke a loko da saƙo. Saboda kykkyawar manufarta da ƙaunar da ta ke yi wa al’umma wajen ganin sun samu nasara da cigaba a rayuwarsu.

Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje zuciyarta a wanke ta ke fesfes a kullum burinta da fatanta shi ne ta taimaki jama’a ta gina al’umma domin cigabansu da cigaban ƙasa gaba ɗaya.

Wannan kaɗan kenan daga cikin irin namijin ƙoƙarin da Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje ta ke yi a fannoni daban-daban kan rayuwar al’umma wanda hakan ne ya sanya na zaɓe ta a matsayin gwarzuwata ta shekarar 2020.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: