Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuNLC zata kure karfinta kan El-Rufai don kada sauran Gwamnonin suyi koyi...

NLC zata kure karfinta kan El-Rufai don kada sauran Gwamnonin suyi koyi dashi

TO FA: Kungiyar Kwadago ta NLC zata kure dukkan karfinta da yin taron dangi kan Gwamna El-rufai don ganin bai yi galaba akansu ba suna fargaban muddin yayi galaba to sauran Gwamnonin ma zasu dauki salonsa

Daga Muryoyi

Kungiyar Kwadago ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta sanya baki a rikicin NLC da Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin Malam Nasir El-Rufai idan ba haka ba abun zai bazu ya shafi duka kasarnan.

Kungiyar Kwadago ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta sanya baki a rikicin NLC da Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin Malam Nasir El-Rufai idan ba haka ba abun zai bazu ya shafi duka kasarnan.

- Advertisement -

A sanarwa mabanbanta da kungiyoyin suka fita kungiyar masu dakon mai na kasa NUPENG da ta maikatan wutar lantarki NUEE, da wata kungiyar kare yanci ta ASCAB sun fitar da sanarwa akai inda NUPENG ta umurci duka mambobinta dake fadin kasarnan su zauna cikin shiri domin a cikin sa’oi kadan zasu iya kiran yajin aiki idan har bukatan hakan ta taso.

Ita kuwa kungiyar ma’aikatan wutar lantarki gargadi tayi cewa sun samu bayani cewa za a iya kawo wuta cikin daren yau a Kaduna saboda haka muddin TCN ta yarda aka kawo wuta a Kaduna to zasu tsunduma yajin aiki na ma’aikatan wutar lantarki a duka kasar.

ASCAB wace babban lauya Falana ke jagoranta kuma barazana sukayi cewa kada hukumar yan sanda ta sake ta bawa Gwamnatin jihar Kaduna goyon baya domin Gwamnan a cewar ta bashi da hurumin kama shugaban kwadago ta kasa NLC Ayuba Wabba da jagororin kungiyar. Sun ce kiran ya zama wajibi ne domin sun ji yadda Gwamnan ya fara shelan neman Wabba ruwa a jallo.

Muryoyi ta ruwaito shugaban kungiyar izala ta kasa Bala Lau ma ya bi sahu inda ya nemi Gwamnatin jihar ta Kaduna da kungiyar kwadago su zauna suyi sulhu domin kawo karshen tirka-tirkar da ake ciki a jihar.
Su ma dai kungiyar Gwamnoni ta kasa da kuma kungiyar Gwamnonin APC duka kira sukayi da a zauna teburin sulhu a tattauna domin kawo karshen wannan yajin aiki dake faruwar a jihar baki daya.

Ana dai samun mabanbantan ra’ayin a inda wasu ke sukar Gwamnan wasu kuma na yaba masa bisa cewa lallai ya kamata Gwamnatin tarayya da sauran jihohin 35 na Nigeria su yi koyi da Gwamnan domin abunda yake yi kowane Gwamna haka ne a ransa amma tsoron kungiyar kwadago ya hanasu aiwatar da abunda ya kamata

“dama dai kungiyar kwadagon ta lashi takobin kure karfinta a kan Gwamnan ta hanyar yi masa taron dangi domin ganin bai yi nasara akansu ba suna masu cewa da zaran ya samu nasara to duka Gwamnoni da Gwamnatin tarayya ma zasu dauki salonsa. Hakan tasa sauran jihohin ma sun fara turo nasu maikatan domin kara yawa su yaki Gwamnan iya karfinsu

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: