Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuRasuwar kanina ta ishemu wa'azi kudi baya iya sayen rayuwa -inji Ɗangote

Rasuwar kanina ta ishemu wa’azi kudi baya iya sayen rayuwa -inji Ɗangote

Daga Muryoyi

Babban dan kasuwa kuma shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana yadda ƙaninsa, Sani Ɗangote ya rasu a gabansa a wani asibiti dake Miami a kasar Amurka.

Ɗangote ya bayyana cewa a gabansa da maihaifiyarsu, da ƴaƴan Sani Allah yayi masa cikawa, suna ji suna gani babu abunda zasu iya.

Ya ce da su ka je asibitin, a lokacin da a ke duba marigayin, likitoci sun faɗa musu cewa nan da awa ɗaya margayin zai rasu.

- Advertisement -

Dangote wanda ke jawabi a lokacin da ya tarbi Jagoran APC na kasa Bola Ahmed Tinubu da Kakakin majalisar dokokin ta kasa Femi Gbajabiamila a yayin da suka je yi masa ta’aziyya yau Juma’a a Kano ya ƙara da cewa lokacin da marigayin ya ke kwance an jona masa na’ura, “abin baƙin ciki da ciwo shine muna kallo ta na’ura har ya rasu. Wannan abu da tashin hankali ya ke.

Amma haka Allah Ya tsara. Kuma kowa zai rasu. Ba wanda ya san wanene gawar fari. Ko mai kuɗi ko talaka. A matsayin mu na musulmai, mun yi imani da mutuwa inji shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sani Ɗangote, wanda shine mataimakin rukunin kamfanoni Ɗangote, ya rasu a wani asibiti da ke Miami a kasar Amurka.

A nashi jawabin, Tinubu ya baiyana cewa kuɗi ba zai iya siya rayuwa ba, inda ya ce idan mutuwa ta zo ba abinda a ka isa a yi.

Ya yi kira ga Dangote da sauran dangin marigayin da su dage da yi masa addu’a, in da ya ce ya zo Kano me domin yin ta’aziyar mamacin.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: