Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuRayuwar Hostel –Sako zuwa ga ‘Yan matan Jami’a

Rayuwar Hostel –Sako zuwa ga ‘Yan matan Jami’a

Daga Abubakar Shuaibu Sytees

 

Sau da yawa na kan so na kasance mai son rubutu musamman da yare na da na taso naga iyayen mu da community nayi don shine ya fi sauki mika sako ta hanyar da ya dace don kuwa shine hanyar da sako zai kai kunnuwa da ya kamata. A daren yau Laraba, 6th January, 2021 bayan farkawa na barci wasu abubuwa suka fado min a rai da ya saka ni yin wanga rubutu mai take a sama.

Rayuwa Mace wata irin rayuwa ce mai hatsarin gaske wacce cikin kankani lokaci zata iya wargajewa sakamako ‘kan’kani sakaci da ko ita da kanta zatayi ko kuma Iyayenta da wasu magabata. Ko da kuwa an gyara daga baya sai wannan abu yayi tasiri akanta, Iyayenta ko iyali masu zuwa.

 

 

Akwai wani Irin rayuwa da ‘yan mata suke gabatarwa acikin dakunan su na kwana (Hostel) ko dakunan da ake kamawa awaje makarantu Wanda a tunanin su ba wata matsala ba ce.

- Advertisement -

A yanayin tsarin dakunan kwana na makarantun mu na gwamnati da ma sauran wasu private Schools din, A kan samu dakuna ne Wanda zaka ga yana daukan Mutane masu yawa acikinsa Wanda ya hada da Mutane daban-daban kuma masu Addini (Religion) da Al’adu mabanbanta. Wanda ni abun da na dauka mara kyau kila wani/wata is normal agare(shi/ta).

 

Kar na cika ku da surutu amma zan danyi tsokaci kadan akan wasu abubuwa da suke faruwa a dakunan kwana na mata da wasu matsaloli da suke haifarwa base on the experience da nike dashi a kalla na Shekaru takwas acikin Jami’a tun ina Dalibi har zamana Ma’aikaci acikinta Kamar haka:

 

RAYUWAR ACIKIN DAKUNAN KWANA

 

A duk lokacin da ‘ya mace ta ke cikin daki ta kan so tayi yadda taga dama ma’ana yanayi walwalanta da Irin shigarta (Mode of Dressing). Zaku ga budurwa ta saka irin kayan da taga dama wanda a tunaninta duk mata ne baki daya. Ko da kuwa wanka zata shiga bayi (bathroom) zaku ga sau da yawa wasu daga cikin su daga su sai towel kai wasu ma daga Pant sai rigar nono. Wasu zasu tambaye ni to menene aciki? Tabbas wannan shiga nata shine mafari tsunduma ta acikin taskun rayuwa. Ta yaya hakan zai kasance? A yanayin da muka tsinci rayuwa ta Digital Age ko nace Computer age wanda kusan kowa na da duniyan sa a hannunsa (Mobile Phone) akwai shaidanun mata, yan madigo ko nace Kawalen mata acikin Su da zasu zama matsala agaresu.

A yadda labarin yazo min shine Wasu matan sai su mamaye ki suyi miki Video a irin wannan shiga da kikayi wanda yike nuna tsaraicin jikinki baki daya. Ya danganta da wacece tayi wannan Video. Idan kawaliya ce zata siyar da Video wajen abokan huldarta Mazinata sannan sai ta basu hanyar da zasu same ki ta waya ko wani wajen. Za su bijiro miki da zance Zina ta hanyar lumana wanda da ta bijire sai suyi mata barazana da wannan Video nata da sunan zasu yada/watsa shi a duk wani social media platforms wanda a dalilin haka da yawa acikin mata zasu gwammace su amince da hakan da ace an yada tsaraicin su a duniya.

 

YIN HOTUNA A HOSTEL

 

Sau da yawa wasu mata basa damuwa da yin hotuna acikin hostel acikin ko wacce irin shiga don a tunaninsu wayarsu ce ba wata matsala aciki kuma dukansu mata ne so ba wani damuwa bace. Bazan taba manta lokacin da na taba amsa wayar abokiyar karatu don kallon hotuna. Tambaya da na fara mata shine zan iya shiga? Amsa kuwa da ta bani shine Ehh, amma kada ka kallo ma idonka abunda yafi karfin ka. Ai ko daga bude folder camera dole yasa na kulle da kai na. Saboda wasu hotuna baza su kallu ba. Anan matsala shine da wayar zata kasance daga ita sai ita da an samu sauki amma kuskure shine komai zai iya faruwa, Ko wani/wata da ake ba wayar ya/ta shiga sugani su tura makansu, Ko a sace wayar a gani ko kuma Idan ta lalace ankai gyara wani ya gani ya kwashe su har a samu mai yada su.

 

 

HANYAR MAFI SAUKI DA YAN MADIGO SUKE SAMUN DAMA

 

Da yawa matan Jami’a Suna afkawa wannan fitinah ce ta dakunan kwana, mata ‘yan madigo sukanyi amfani da zaman hostel ta hanyar karkatar da musamman mata masu karanci Shekaru da kuma sababbin zuwa (Jambitos) zuwa irin lalataciya harkarsu a yadda yanxu mafi yawanci Jami’a basa duba Shekaru wajen bada admission na dalibai, Zaa iya Samu yarinya yar 14-15years an bata admission wanda akwai sauran kuruciya a tare da ita gashi ba masu tsawatar wa a kusa.

 

Wasu masu wannan harkar banza sukan fara sha’awar yarinya ta irin sura jikinta da suka gani a yayin irin shigar da ta ke yi acikin hostel ko lokacin hutawa, wanka ko saka kaya. Don mata basu cika jin kunyar junansu ba Kamar ‘Da namiji.

 

Zata iya shiga agaban yar’uwata mace ta saka kaya agabanta ba tare da wani tunani ba. Daganan ne suke amfani da daman su wajen fara yabon wasu sassa na jikinta tana jin dadi har ya kai ga sun fara taba wasu sassa a jikinta da sunan wasa har zuwa lokacin da zasuyi nasara daura ta akan hanya. Su kanyi amfani da nuna ma yarinya ba wani matsala aciki don baza asan tana aikatawa ba tunda baza tayi ciki dasauransu, Shiyasa yana da kyau duk yarinya da ta ke rayuwa hostel kada ta cika barin sauran yan’uwanta mata sugane abubuwan da kan iya jawo mata sha’awa, lokaci period nata dasauransu don suma sukanyi tasiri sosai wajen samun dama saka su acikin fitinah batare da sunyi la’akari da hakan ba.

 

A karshe ina kira da Iyaye, hukumomin makarantu, Kungiyoyin addinai da sauransu wajen jawo hankulan mata da maza don koyar dasu irin rayuwar da ta dace a duk inda suka samu kansu, Sannan Iyaye su tarbiyanta da yaransu akan tsoron Allah don da yawa iyayen yanzu sunfi saka ma yaransu tsoron su fiye da na Allah (SWT) Shiyasa da yaransu sun samu dama zasu jefa kansu mawuyacin hali.

Anan zan tsaya a yau amma bayan lokuta zan duga sako muku wasu rubututuka na musamman akan rayuwa. In Shaa Allah ina nan zanyi sabon rubutu mai taken “Kan ta Waye – Muyi-muyi mu amfana: Rayuwar sabuwar Daliba a Jami’a da Samarinta.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: