Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuRUSAU: Wata mata ta yiwa El-Rufai kazafi

RUSAU: Wata mata ta yiwa El-Rufai kazafi

TA YI WA EL-RUFAI KAZAFI: Wata mata ta gudu ta boye kanta bayan da ta gano ashe ba El-Rufai ya tura a rusa gidan makwafcinta ba bayan ita kuma tayi bidiyo tana kuka cewa Gwamnan ne ya tura a rusa gidan

…ashe gidan saman da matar ta nuna ana rusawa a bidiyon gidan wani soja ne da ake rikici akai ba Gwamnan ne ya sa a rusa ba kamar yadda matar ta ke ihu tana fadi a cikin bidiyon

Daga Muryoyi

- Advertisement -

Matar da tayi wani bidiyo tana kwarmata ihu cewa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya turo a rusa gidan makwafcinta gashi ana rusawa har ma tana tsoron kada ya fado kan yayanta ashe ba Gwamnan bane ya tura a rusa gidan, yanzu haka dai matar ta boye ta ki yadda ta gana da yan jarida tun bayan da gaskiyar maganar ta fito.

Muryoyi ta ruwaito bidiyon ya yadu sosai a shafukan sada zumunta inda aka nuna ana rusa wani gidan sama kana aka jiyo muryar matar tana ihu tana jawabi tare da alakanta rusa gidan ga Gwamnan.

Wani fitaccen dan jarida Salisu Umar Salinga ya bi sahun lamarin inda ya gano ainihin abunda ya faru. Ashe dai rikici ake yi akan gidan wanda har ta kai ga mai gidan wani Soja mai murabus ya dauki doka a hannunsa lamarin da ya jawo aka rusa gidan.

Muryoyi ta ruwaito yanzu haka maigidan na hannun hukuma kuma batun na gaban hukuma ana shara’a.

Sai dai har yanzu matar taki bayyana kanta tun bayan da gaskiyar magana ta bayyana. Muryoyi zata sako maku cikakken rahoton a cikin bidiyo wanda Salisu Umar Salinga ya hada a tashar talbijin ta Salinga TV.

Sai dai zuwa yanzu ba a san ko Gwamnan zai dauki matakin shara’a kan matar da tayi bidiyon ba wanda ya zaga duniya yanzu haka.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: