Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSamari a rika tsafta, kalli hoton dakin wasu gayu a Kaduna

Samari a rika tsafta, kalli hoton dakin wasu gayu a KadunaDaga Muryoyi

Tsafta abu ce mai matukar tasiri ga rayuwar dan adam wacce ke da tasiri ga lafiyarsa, kuzarinsa kai har ma uwa uba ga addininsa, domin har hadisi sukutun guda akwai wanda ke magana akan “tsafta na daga cikon addini”. Tsafta tana da rassa daban-daban kama daga tsaftar jiki, tufafi zuwa ga abinci da muhalli da dai sauransu.

Hatta wajen hada-hada da mu’amala ta yau da kullum da suka hada da neman aure da zamantakewa tsafta na taka muhimmiyar rawa. Sai dai duk fadakarwar da malamai da jami’an kiwon lafiya ke yi baya shiga kunnuwan wasu mutanen musamman anan yankin namu.

Kofar shiga da kuma katifar da samarin ke kwanciya.

Kamar dai yadda zaku gani a wannan rahoto da jaridar Muryoyi ta hada maku. Wakilin jaridar Muryoyi ya ziyarci dakin wasu samari matasa masu jini a jika, a nan garin Kaduna dake Arewacin Nigeria. Sai dai mun gano ashe duk cika bakin gayun Kaduna da suke cewa su ne sarakuna wajen iya wanka, da tsafta, da caba ado to a wannan karon an kwafsa.


Muryoyi ta fahimci wannan daki da kuke gani wajen kwanan wasu kattin samari ne kuma su ne ke kwana a cikinsa kusan su 4 zuwa 5 sannan kuma babu dan kasa da shekara 17 a cikinsu. Hasali ma akwai wanda a yanzu haka yake shirin angwancewa da zankadediyar budurwarsa. Allah kadai yasan ko ta taba ziyartar wannan juji au a gafarce ni wannan daki.

- Advertisement -Binciken Muryoyi ya nuna daya daga cikin masu kwana a wannan daki Jami’in tsaro ne kuma ya kai shekara 30 da doriya, sannan daya kuma dan kasuwa ne dake aiki a wani katafaren wajen sayar da kaya da yayi fice a Kaduna, dayan da ke bi masa kuma babban mai sana’ar hannu ne wanda yayi fice har yake zuwa gari-gari, jiha-jiha. A takaice dai kunga ba za a ce talauci ne ya jawo wannan kazantar ba.

Kaya baza-baza akan kujera ko kushin sannan sun bari duk kushin din ya fita hayyacinsa
Talabijin, gado a gefe kana gashi nan an watsar da kayyaki da suturu da su takalman sawa ko ta ina ba kyan gani.Kamar yadda kuke gani, ga kayan sawa nan baja-baja a kasa a warwatse, ga kuma kushin nan yayi daka-daka duk ya soma fita hayyacinsa ya yayyage, ga alama net ne a daya daga cikin gadon barcin, amma ba a maganar katifar kwanciya wacce ta fita hayyacinta, ga kayayyaki nan kota ina kamar dakin da tom and Jerry ke wasan buya a ciki ko kuma wajen kwanan dabbobin da basu da gata. Wannan abu har ina?


Muna fata gayun Kaduna za a tashi tsaye wajen kula da tsafta domin ko ba komi tsafta na daga cikin addini sannan Allah da kansa ya fada mana shi mai tsarki ne kuma baya karbar wani abu sai mai tsarki. Kafin rahoto na gaba zamu so yan mata da sauran samarin sauran wajaje su bayyana mana ra’ayoyinsu akan wannan rahoto munsan ba mamaki akwai irin wadannan samari a inda kuke… Muryoyi na nan zuwa…

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: