Sheikh Gumi yace ya dawo rakiyar yan bindiga tunda an ayyana su yan ta’adda

Daga Muryoyi

Fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, yace ba zai sake yin magana ko shiga neman sulhu da yan fashin daji ba domin Gwamnati ta riga ta ayyana su a matsayin yan ta’adda.

Shehin Malamin a tattaunawarsa da majiyar Muryoyi yayi mamaki me yasa Gwamnati tayi saurin ayyana su a matsayin yan ta’adda bayan kuma sun nuna a shirye suke ayi sulhu.

Ya ce kofar da tayi saura shine malamai su shiga tsakani to amma kuma yanzu ba sauran hanyar tuntubarsu saboda Gwamnati ta ayyana su a matsayin yan ta’adda,
Magana dasu tamkar taimakawa yan ta’adda ne inji Dakta Gumi

- Advertisement -

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: