Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuShugaba Buhari ya rubutawa INEC wasika ta neman shawara kan zaben yar...

Shugaba Buhari ya rubutawa INEC wasika ta neman shawara kan zaben yar tinke

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soma tuntubar masu ruwa da tsaki su bashi shawara da ra’ayinsu kan ya saka hannu ko kar yasaka akan sabuwar dokar gyaran zabe da majalisun tarayya suka aike masa wacce ta bukaci a rika yin yar tinke, wato kato bayan kato, hajiya bayan hajiya a lokutan zaben fidda Gwani a kowace jam’iyya a Nigeria.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito cikin wadanda Buhari ya rubutawa wasikar neman shawara har da hukumar zabe ta kasa INEC, karkashin Farfesa Mahmoud Yakubu da Ma’aikatar Shara’a ta Nigeria karkashin Abubakar Malami SAN da wasu da dama.

Zuwa yanzu dai ana ta kai ruwa rana a fagen siyasar Nigeria dangane da wannan doka wacce Gwamnoni ke adawa da ita su kuma yan majalisar dokoki ke kokarin ganin shugaban kasar ya sanya mata hannu. Gwamnonin suna ta kamun kafa da magiya gun duk wanda suka san zai iya lallaba Buhari akan kada ya amince da dokar.

- Advertisement -

Me zai faru idan shugaban kasar yaki amincewa da dokar?

Majalisar dokoki ce ta kirkiri dokar a ranar 9 ga watan Nuwamba 2021, sannan suka aika wa shugaban kasa domin ya sanya hannu a ranar 19 ga watan Nuwamba, A bisa doka ya zama wajibi ga shugaban kasar ya bayyana ra’ayinsa na yarda ko rashin yarda da dokar daga nan zuwa ranar 19 ga watan Disamba 2021 wato kwana 30 cif-cif.

Idan bayan kwana 30 shugaban kasar bai saka hannu a dokar ba kuma yan majalisar suka ji basu gamsu ba, to suna da damar yiwa kudurin dokar kiranye sannan su yi kuri’a a tsakaninsu, idan aka samu 2 bisa 3 na sanatoci da 2 bisa 3 na yan majalisar dokoki ta tarayya suka amince da dokar to shikenan ta zama doka koda kuwa shugaban kasar bai saka hannu ba.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: