Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuShugaba Buhari yace Nigeria bata da dalilin shigo da abinci daga wata...

Shugaba Buhari yace Nigeria bata da dalilin shigo da abinci daga wata kasa

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bai ga dalilin da zai sa a rika shigo da kayan abinci daga wata kasa ba saboda Allah ya horewa Nigeria dumbin albarkatun kasa da za a iya noma komi a ciki,

Shugaban a don haka yayi kira ga manoma da hukumomin noma su hada kai tare domin yin abunda ya dace kasarnan ta kara dogara da kanta. Abinci ya wadata.

Shugaban kasar ya kuma kalubalanci Jami’o’in Nigeria baki daya da su tashi tsaye wajen yin amfani da dumbin ilimi da basirar da Allah ya huwace masu, su lalubo maganin cutar korona domin itama Nigeria ta yi nata allurar rigakafin, wanda zata kare kasarta da yan kasarta.

- Advertisement -

Buhari wanda ke magana a yayin bikin yaye dalibai a jami’ar tarayya dake Dutsin-Ma (FUD-MA) jihar, Katsina da kuma jami’ar Michael Okpara University of Agriculture Umudike (MOUAU), jihar Abia.

Muryoyi ta ruiwaito shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin ministan Noma, Dr. Mohammed Abubakar a MOUAU, da karamin ministan ilimi, Mr. Chukwuemaka Nwajiuba a MOUAU, ya kalubalanci Jami’o’in kasar nan da su yi bincike sosai su lalubo hanyoyin da Nigeria zata rika samun kudaden shiga da kuma dogaro da kanta a madadin dogaro da albarkatun mai kadai.

Ya ce lokaci yayi da kowa zai yi abunda ya dace domin bunkasar tattalin arziki da cigaban kasarnan

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: