Shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey yayi murabus
Daga Muryoyi
Shugaban kamfanin sadarwar zamani Twitter Jack Dorsey yayi murabus daga mukaminsa na shugabancin kamfanin tsawon shekara 16.
A wata sanarwa Muryoyi ta ruwaito Mista Dorsey wanda aka fi kira da Jack ya sanar da nada Mista Parag a matsayin sabon shugaban kamfanin na Twitter daga yau.
- Advertisement -
Parag ma’aikacin Twitter ne da ya jima a kamfanin yana hidima a ciki. Mutum na biyu da kamfanin ya nada ya jagoranci hukumar gudanarwar kamfanin shine Bret Taylor
Jack yace shine ya yanke shawarar yin murabus domin ya koma gefe ya cigaba da wasu harkallarsa.
Ana dai danganta matsin lamba ce da Tuwita ke fuskanta a sanadiyyar Jack wanda kasashe dayawa ke kullace dashi ciki har da Nigeria saboda irin yadda yake fitowa kai tsaye yana goyon bayan masu tsageranci