Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSirruka 7 da karas ke dauke dasu

Sirruka 7 da karas ke dauke dasu

Tare da Aisha Aliyu Shanono

Mutane da yawa na amfani da Karas wasu na ci danye wasu kuma suna amfani da shi wajen kawata girki amma akasarin mutane basu san amfanin shi a jikin dan Adam ba.

Karas na dauke da sinadarai da dama domin yana taimakawa wajan kara lafiya da kuma kare mutane daga wasu cututuka kamar haka.

1. Ciwon ido: Karas na dauke da sinadarin vitamin “A” wanda yake karfafama idanu wajan gani.

- Advertisement -

2. Gyaran fata: Karas na dauke da sinadarin ‘carotenoids’ wato sinadarin dake haskaka fata ya sanya ta tayi kyau

3. Ciwon daji: Karas na dauke da sinadarai masu dumbin yawa, wanda ya hada da “phytochemical” da ke yaki da cututukan daji, yana kuma karfafa garkuwan jiki da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji

4. Kwarin Kashi: Sinadarin da karas ke dauke da shi yana kare kwayoyin halita daga cututuka yana kuma inganta lafiyar ‘kashi

5. Rage kitse: Idan mutum yana bukatan rage kitsan dake jikin shi to ya luzumci cin danyen karas domin yana dauke da sinadarin “lectin” mai taimakawa wajen rage kitse.

6. Ciwon Baki da hakora: Cin danyan Karas na taimakawa wajan magance cututukan baki da hakori kuma yana bada numfashi mai inganci

7. Ciwon hanta: Karas na dauke da “beta carotene” da “vitamin A” wanda suke inganta lafiyar hanta da ba ta kariya daga kamuwa daga wasu cututtukan.

Karas na taka muhinmiyar rawa a jikin dan adam kuma dama yanzu lokacin shi ne da fatan za a lazumci cin karas, mai gida da uwar gida …rugakafi dai aka ce ta fi magani. Ku biyo mu a shiri na gaba a cikin filin JI KA KARU tare da ni yar’uwar ku Aisha Aliyu Shannon domin jin wani sabon maudu’in!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: