Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuTabbas Maryam tayi wa kanta fada da tayi aure yanzu ta kaucewa...

Tabbas Maryam tayi wa kanta fada da tayi aure yanzu ta kaucewa rudin duniya -YSA

Daga Muryoyi

A ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba aka daura Auren fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Wazeery wacce aka fi sani da Laila a cikin shirin Labarina.

Rahotanni sun nuna jarumar tayi amarce ne da tsohon dan wasan Super Egale Tijjani Babagida.

Muryoyi ta bi ra’ayoyin jama’a dake tofa Albarkacin bakinsu akan auren wanda akayi shi a boye,

- Advertisement -

Wani mai suna Yusha’u S Abdul ya ce
“Maryam Wazeery tabbas tayiwa kanta fada datayi auren ta ta kaucewa rudin duniya alokacin da tauraruwar ta take kan haskawa, kafin tauraron ya dusashe tazo tana neman muji alokacin kuma neman mujin ya gagara.

Yanada kyau mata masu shirya harkan fina finai na KannyWood su shiga taitayin su, su sani cewar rayuwar ya mace da zaran ta haure shekaru ashirin da biyar ta tafi gangara, sannan kuma duk haskawan ki bai wuce shekara biyar ansoma gajiya dake daganan kuma wata zata zo kina kallo ta maye gurbin ki.

Fatan mu shine Allah Yasa wannan aure ace gwanda da akayi, Allah Ya bata zaman lafiya da zuri’a masu albarka.”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: