Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuTinubu bashi da takardar shaidar kammala karatu ko daya, bai cancanta da...

Tinubu bashi da takardar shaidar kammala karatu ko daya, bai cancanta da takara ba

Daga Muryoyi

Muryoyi ta ruwaito Babban jigo a jam’iyyar PDP, Olabode George, ya bayyana cewa kwata-kwata tsohon Gwamnan jihar Lagos, Bola Tinubu bai cancanta da shugabancin Nigeria ba ta kowace fuska.

Mista George, a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise a yau Laraba ya ce Tinubu ya yi badakala da kudaden jihar Lagos yadda yake so sannan kowa yasan yadda yake amfani da kamfaninsa na Alpha-Beta yana kwashe kudaden Lagos dashi. A cewarsa duk wata sai an baiwa Tinubu Naira Bilyan 30.

- Advertisement -

Sannan kuma a cewar Mista George din Tinubu bashi da takardun makaranta gaba daya. “Na saka kyautar kudi ga duk wanda ya kawo shaidar takardar karatun Bola Ahmed Tinubu na firamare ko sakandare ko Jami’ar da yayi”

Muryoyi ta ruwaito jigon PDP yana cewa a 1998 ko 1999 Tinubu ya kasa kare kansa game da takardun da ya baiwa hukumar zabe INEC. Yace yayi karatu a  Government College Ibadan da kuma Children Hope School a Ibadan amma da aka bi diddigi sai aka samu karya ne bai yi makarantar ba sai ya wayince yace wai wani Afikuyomi ne ya wakilceshi.

Ya kara da cewa da ace kasar da take abunda ya kamata ne ma da yanzu EFCC sun tasa Tinubu a gaba domin bankado badakalar da yake yi da arzikin jihar Lagos ya bi ya tatse ta tass. “Ni duk ranar da akace mutum irin Bola Tinubu ya amshi ragamar kasarnan to ko ta halin kaka ne sai na cenza kasa”

Kuma Bode George ya ce duk binciken da akayi an kasa gano abokanan karatun Tinubu

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: