Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuTsohon limamin Ka'aba ya fito a fim din talla

Tsohon limamin Ka’aba ya fito a fim din talla

Daga Muryoyi

Miliyoyin musulmi a fadin duniya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu sakamakon ganin tsohon Limamin masallacin Ka’aba Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani a cikin wani fim na tallar wata kolokuwar wasanni da kasar Saudiyya da za ayi a birnin Riyadh mai suna ‘Combat Field’ zone of Riyadh Season 2021 

Ministan harkokin Nishadi na Saudiyya, ta hannun Turki al-Sheikh ne ya soma dora bidiyon mai tsawon minti 2 da dakika 41 a shafinsa na Tuwita, inda aka ga Shehin Malamin ya fito tare da sauran jarumai da taurarin fina-finai da yan kwallo suna tallar kalankuwar.

A cikin bidiyon an nuna sojoji a fagen yaki dauke da makamai suna shirin fafatwa.

- Advertisement -

Jim kadan da dora bidiyon ne sai Shehin Malamin yayi barkwanci cewa “Kuna ganin zan dace da Hollywood kuwa?” Sai dai dubban jama’a sukayi masa ca wasu suna bai dace ba wasu kuma na addu’ar Allah ya shirya a yayinda wasu ke yaba masa.

Dama dai ko a 2018 sai da Adil al-Kalbani ya sha suka saboda ganinsa da akayi a wajen bude gasar karta a birnin Riyadh, har ma dai aka ganshi rike da karta kamar yana bugawa tare da wadanda suka shirya gasar.

Sheikh Adil bin Salem Al-Kabbani

Wanene Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani?

A binciken da Muryoyi tayi ta gano cewa Shehin Malamin mai kimanin shekara 60 da doriya babban malami ne a kasar Saudiyya wanda ya kafa tarihin zama bakin fata na farko da ya taba yin limanci a masallacin Ka’aba

Kuma an haifeshi a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a ranar 25 ga watan Ramadan a shekarar 1378 AH (Hijiriyya), a 1984 yayi aiki a tashar jiragen sama na kasar Saudiyya sannan yayi limanci a manyan masallatai a kasar da suka hada da Riyadh Airport Mosque, King Khalid Mosque da Salah al-Din Mosque da dai sauransu.

Ya taba cewa yayi mafarki ya zama limamin masallacin Ka’aba, kuma cikin ikon Allah sai gashi Sarki Abdallah ya nada shi a cikin wadanda suka ja sallar Tarawi a masallacin Ka’aba a 2008 (shekara 2 da yin mafarkin nasa).

Tarihin rayuwarsa dai kamar yadda Muryoyi ta ruwaito ya nuna matansa Biyu da ya’ya 12.

Malamin na tada kura sosai a Saudiyya saboda ra’ayoyinsa, kodayake dai mabiyin akidar Sunnah ne kuma yana da murya da kira’a mai dadi idan yana karatu amma duk da haka ana yi masa kallon ya cika wayewa, sannan bashi da zurfin ilimin addini.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: