Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWani matashi ya kashe mahaifinsa yana cikin bacci a jihar Edo

Wani matashi ya kashe mahaifinsa yana cikin bacci a jihar Edo

Daga Muryoyi

A yayinda ‘yaya nagari ke bikin iyayensu ta hanyar sanya hotunansu da saya masu kyaututtuka, cen kuwa  a jihar Edo Yan sanda ne suka kama wani yaro dan shekara 13 mai suna Abubakar bisa zargin kashe mahaifinsa dan shekara 79 mai suna Malam Sariakhi Oronsaye yana cikin bacci.

Manuniya ta ruwaito matashin yayi amfani da gatari wajen sassara mahaifin nasa har ya mutu a ranar Lahadi da ta gabata a Egbon Estate dake garin  Evbuotubu, a Benin, babban birnin jihar Edo.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, SP Kontongs Bello dama a satin da ya gabata sai da margayi Oronsaye ya kai karar dan nasa ofishin yan sanda na Evbuotubu saboda yaron yana yi masa barazanar kisa amma kuma sai daga baya tausayin da da mahaifi tasa ya janye karar yace yansanda su bar yaron ashe kuwa zai je ya kashe shi.
Iyalai da yan’uwan wanda ake zargin sun ce bashi da wata lalura ta tabin hankali lafiyarsa garau.

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: