Saturday, June 10, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWani tsohon soja yayi garkuwa da dan makwafcinsa a Kaduna

Wani tsohon soja yayi garkuwa da dan makwafcinsa a Kaduna

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta kama wani Soja, Sani Galadima dake zaune a Badarawa da wasu mutane 3 bisa zargin yin garkuwa da yaron makwafcinsa, Muhammad dan kimanin shekara 6, suka kashe shi bayan an biyasu kudin fansa har Naira miliyan Biyar (5,000 000).

Abun takaici ma shine Manuniya ta ruwaito Sani Galadima wanda ake zargi da sace yaron har ziyartar mahaifin yaron Alhaji Kabiru Magayaki yayi lokacinda ake tsaka da neman yaron inda yayi masa jaje tare da addu’ar Allah ya tona asirin masu garkuwar “ashe kuma shine mai garkuwar”

Muryoyi ta ruwaito asirin Sani ya tonu ne bayan da wani mazaunin unguwar ya hangi shi Sanin rike da yaron a wata tashar mota a jihar Kano inda ya kira mahaifin yaron yake sanar dashi har ma ya labe ya dauki hotonsa ya turawa Baban Yaron domin shaida.

“Mahaifin yaron sai ya jinkirta daga maganar domin wanda ake zargin kani ne ga tsohon kansilan Badarwa, Muhammad Galadima, sannan anyi zaton bayan an biyasu kudin fansa zasu maido yaron amma sai aka ji shiru har bayan kwana 2 da biyan kudin lamarin da ya harzuka mahaifin yaron”

- Advertisement -

Bayan wanda ake zargin ya dawo Kaduna sai yan sanda suka kamashi inda yake bayyana cewa ya kashe yaron sun jefar dashi a wata lamba tu a cen jihar Kano, da aka tambaye shi dalilin kashe yaron bayan an biya kudin fansa sai yace “Yaron ya gane daya daga cikin su wani Nazifi wanda shine ya riko wa yaron hannu daga gida ya kawo ma shi Sani inda shi kuma ya dauke shi zuwa Kano ya boye”

Muryoyi ta gano shi Nazifi wani dan aiki ne a gidan da yaron yake yawan zuwa yin wasa, kuma shine ya dauko masu yaron ya bawa shi sojan inda shi kuma ya dauki yaron ya kaiwa abokinsa a cen Kano suka boye shi har zuwa lokacinda suka kashe shi bayan sun amshi kudin fansa amma suka gane cewa yaron ya gane wanda ya fara dauko shi daga gida.

Sai dai dukkaninsu suna hannun yan sandan jiharsa Kaduna ana cigaba da bincike.

KARIN BAYANI: A wani bincike da jaridar Muryoyi ta yi ta nago cewa Sani korarren soja ne, bayanai sun nuna an koreshi daga soja kimanin shekaru 4 da suka wuce binciken farko ya nuna an koreshi ne daga soja bisa laifin hada baki da yan bindiga ko kuma fashi da makami.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: