Wata amarya a Kano ta rasu ana shirin kai ta dakin ango (kalli hotunan)

Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun: Rai bakon duniya Allah ya yiwa Khadija Kassim rasuwa wata amarya da aka daura aurenta ranar Lahadin da ta gabata 27 ga watan Disamba a garin Bichi.

Manuniya ta ruwaito margayiyar yar kimanin shekara 23 da haihuwa ta fada rashin lafiya ne jim kadan da kammala shagulgulan auren ta har ma ana shirin kai ta dakin angonta Malam Usman.

Sai dai ganin ciwon ya tsananta ne sai aka dauke ta zuwa asibitin garin Bichi inda likitoci suka fara duba har zuwa safiyar yau Laraba inda rai yayi halinsa.

- Advertisement -

Wata kawar margayiyar, Aisha Aliyu Usman wacce ke cike da alhinin rashin Khadija ta shaidawa Manuniya cewa “Anayi Janaizarta yanzu da misalin karfe 12:30 a kofar gidansu dake bayan Masallacin Juma’a na garin Bichi”

Amarya da angonta Usman
Margayiya Khadija yayin bikin kaiye day na auren nata

Tuni dai yan’uwa da abokan arziki suka shiga shafukan sada zumunta suna nuna alhinin rashin wannan baiwar Allah

Tuni dai yan’uwa da abokan arziki suka shiga shafukan sada zumunta suna nuna alhinin rashin wannan baiwar Allah

Kamala Namowa Bichi
Ibrahim yayan amarya
Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: