Wata annoba dake son bullowa a garin Damaturu jihar Yobe

Daga Manuniya
Rubutawa Mahmud A. Kayeri

Zakaga Yara sunsaka KAYA (dressing) na yan DABA suna goge sabbin wukake akan kwalta, duk suna hakanne domin kwoikoyo ga wani bawon Allah dan wani online hausa film, da ake masa lakabi da “ABALE”

A WANI FANNI KUWA

MASU FADA AJI GUDA 8
1. Jami’an tsaro
2.Masarauta
3. Iyaye
4. Matasa
5. Malamain addinai
6. Gomnati
7. Yan Kasuwa, Bankuna da Companunuwa
8. Alkalai da Loyoyi

- Advertisement -

Dukkan wadanda na lissafa na iya fada aji amma dukkansu sun zura ido suna kallo, wasu na daukansa a zaman yara na nishadi, Wasu na sa a zaman gayu, Wasu ma dariya abun ke basu, wasu cewa suke bikin sallah ne kawai.

TAMBAYOYI 8

1. KO KUNSAN wasu jahohi da ake Dabanci Sara-Suka/ Kalare da ire-iren haka suka Fara?

2. KO KUNSAN SIYASA na tankaromu? bakwaga kaman bata gari zasu iya amfani  dasu (yaran)

3. KO KUNSAN  yarannan kullum na mallakan makamai da nifin suna kwaikoyon dan film?

4. KO KUNSAN idan mutum nada kayan aiki dole watarana ya gwada aiki dashi? Hanya Mai kyau KO Mara kyau.

5. KO KUNSAN Laifin Farkone ke da wuya? da zaran kayi na fari na biyu bai baka wahala.

6. KO KUSAN yaran da suka kashe Abubakar UBA sunjima suna kananan laifi ba’a daukan kwakkwaran mataki ? hakan ya basu karfin gwoiwan rubanya aikinsu .

7. KO KUNSAN kannenmu mata basu da tsaro idan aka tafi a haka?

8. KO KUSAN idan annoba tazo ba ruwanta da a gidansu su wane aka fara ?

SHAWARA 8 KO WANI SHAWARA YA HAIFI 3

1. JAMI’AN TSARO yakamata su dauki dabi’u uku (3)

i. yakamata kuna bada fuska ga mutanen gari da bibiyansu domin samun information akan abunda ke faruwa a gari..

ii. Idan kuka samu information a wajen mutum karku bashi wahala.. e.g. sau diyawa zaka kai labarin faruwan abu amma sai kasamu laifi na kokarin komawa kanka, wannan na kashewa mutane hanzari wajen kai rahoto.

iii. Ana kokarin boye information na Wanda ya kawo labari ga jamiyan tsaro saboda tsaronsa .. Gudun kar wadanda yakai labarinsu su masa illa.

2. MASARAUTA yakamata su dauki dabi’a guda uku (3)

i. Cire lokaci domin zama da matasa,iyaye, malamai da duk Wanda suka chanchanta akan abubuwan dake faruwa ba sai ta jira matasa sunzo ba ita masarautan ta gayyacesu..
ii. Ziyara lungu da sako na inda take karkashen masarautan domin ganewa ido meke faruwa a kasa
iii. Hada taruka domin tunatar da matasa akan al’adun gargajiya.

3. IYAYE yakamata su dauki dabi’u uku (3)

i. Kula da tarbiyansu tare da kula da suwaye abokansu tun suna tasowa..
ii. Sasu a makaranta da nema musu sana’an dogaro da kai..
iii. Jan kunne ga yara ko dankane shi KO na makwabcinka ….

4. MATASA yanada kyau mudau dabi’u uku(3)

i. Neman ilimi a makaranta da wajen makaranta.. Da yin Sana’an dogaro da kai
ii. Haduwa akai – akai domin tattauna matsalolin da ke damun garin baki daya…
iii. Nemawa abokanmu da suka shiga matsala mafita, ta hanyan hadakai idan anga yanaso ya lalace a jawosa jiki a samo wata hanya ta daidai da za’a daurashi …

5. MALAMAI su dauki dabi’u uku(3)

i. Jayo matasa a jiki da rage kyaman matasa da suka lalace domin ganarsu hanyan da yadace subi….
ii. Ziyartan Masarautu, Gomnati , Jami’an tsaro domin basu shawara akan al’amuran dake wakana a gari dakuma basu karfin gwoiwa idan sunakan daidai….
iii. Tara mutane domin addu’oi akai-akai domin neman zaman lafiya da cigaba..

6. GOMNATI yakamata su dauki dabi’u uku (3)

i. Bada hadinkai ga jami’an tsaro tare da tura wakilanta lungu da sako, sannan a dunga tambayansu ya ake ciki? basai anjira sunkawo sako bah idan akaji shiru
ii. Idan tazo bada tallafi ko koyawa matasa Sana’a ta tabbatar tayi adalci sannan tana duba meye matsalolin al’uman kafun kawo musu dauki. e.g. kabawa saurayi kyautan SANITARY PADS kaga ba’a bada ita a huruminta bah…..
iii. Tabbatar da andauki matakin  gaggawa ga duk wanda yayi laifi na kusa ko nesa da gomnati…

YAN KASUWA BANKUNA DA KAMFANONI etc yakamata su dauki dabi’u uku(3)

i. Hadakai domin daukan nauyin karatu ga yara domin karsu lallace a gari
ii. Hada taro ko zuwa wajen taro domin bada shawara ga matasa akan dogoro da Kai… Hakan zai iya rage yawon barayi
iii. sa hannu a duk abunda zai kawo cigaba… e.g. a wasu garuruwa zakaga bank,yan kasuwa etc suna project amma anan ko oho…

8. ALKALAI DA LOYOYI yakamata su dauki dabi’u uku(3)

i. Bada fuska ga al’umah domin fahimtar ya rayuwa ke tafiya…. Masu Shari’a da dama basa yarda su shiga cikin mutane(daga wajen aiki sai gida wasu ko sallah a gidansu sukeyi) hakan nasawa ba lalle su fahimci ya duniya take a wajeba … Sanin yadda yanzu al’umah take kuwa zai taimaka Sosai…
ii. Barin gaskiya a huruminta domin idan yau ka kare Wanda  yayi ta’addanci akan wani toh ta yuwu gobe akanka ko kan waninka zaiyi.. tare da hukunci mai tsauri ga Mai kokarin ta’addanci ko kawo husuma hakan zai zama izina.
iii. Koyar da al’umah Shari’a da yadda take aiki  ( ya ake shigar da Shari’a dakuma right na mutum ya zaiyi ya kwato ) za’a iya wallafa littafi kuma ana hada taro domin wayarwa mutane Kai……

DAGA KARSHE
Ina Kira ga dukkannin al-ummah da mu’ajiye banbance – banbance dake tsakaninmu (PDP, APC etc.. da kuma banbancin Yare) domin idan annoba ta taso babu ruwanta da duk wannan… Kowane zaiji a jikinsa … Muyi addu’oi sosai domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba mai daurewa….

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: