Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWata daliba a jam'iar Yar’adua ta sha guba saboda saurayi ya yaudare...

Wata daliba a jam’iar Yar’adua ta sha guba saboda saurayi ya yaudare ta

Daga Muryoyi

Wata dalibar aji Uku (300-Level) a jam’iar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina ta sha man wanke hannu da fiya-fiya saboda saurayinta yace ba zai aureta ba an saka masa ranar aure da wata budurwar

Wani babban ma’aikaci a jam’iar ya shaidawa Muryoyi cewa sunan dalibar Ummi kuma a fannin koyon ilimin zamantakewa take wato Sociology.

Muryoyi ta ruwaito lamarin ya faru ne a daren jiya Juma’a, bayan saurayin dalibar ya iske ta a makarantar ya shaida mata halin da ake ciki. Rahotanni sun nuna dalibin yana ajin karshe ne wato 400 yazo “Clearance” a makarantar shine ya neme ta yake fada mata cewa an sanya masa rana da wata don haka soyayyarsu ya zo karshe da ita”

- Advertisement -

Wata dalibar makarantar wacce ta bukaci a boye sunan ta ta shaidawa majiyar Muryoyi cewa ‘sun ga ta shiga dakin ta a Hostel kafin su farga har ta kwankwadi man wanke hannu (handsanitizer) kuma nan da nan jiri ya dibe ta ta zube kasa.

Daga bisani aka kaita asibitin makarantar kodayake har kawo yanzu da muke kammala wannan rahoto bata cikin hayyacinta. Kazalika anki bayyana cikakken sunan dalibar da Saurayin nata.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: