Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYadda zaka samu ladar Hajji daga gidan ka kamar ka hau Arfah

Yadda zaka samu ladar Hajji daga gidan ka kamar ka hau Arfah

  • Daga Abdullahi Salihu Abubakar
    Abuja – Zulhijja 09, 1442AH

YININ ARAFAH: IKHLASI…TAWALI’U…NEMAN GAFARA!

1. Jama’a, YININ ARAFAH yini ne mai cike da albarka da rahama da kuma gafarar Ubangiji. Bude zuciyarka, cike ta da madarar ikhlasi, shayar da ita nonon tawali’u da hakuri, NEMI GAFARAR ALLAH.

2. YININ ARAFAH yini ne mai cike da falala daga Allah. Kada ranka ya baci baka samu zuwa aikin Hajji ba. Raya dararenka, azumci yininka, lazimci harshenka da zikiri da karatun Kur’ani. A shirye Allah yake ya biya maka bukatunka.

- Advertisement -

3. YININ ARAFAH yini ne da Allah ke alfahari da bayinsa mahajjata da suke tsaye wurin suna ta neman gafararsa.

4. YININ ARAFAH yini ne da Allah ke gafarta zunuban shekaru biyu cur, idan ka azumce shi babu kwange. Idan mace ce ke ba ki cikin yanayin da za ki iya azumi, kambama kwadayinki ga rahama da gafarar Allah, kwallafa ranki ga ladar Ubangiji, mawadaci ne shi wanda babu kamarsa; yana iya baki ladar wadanda suka yi azumin.

5. A cikin YININ ARAFAH ne Allah ya cika addinin nan, ya cika ni’imarsa garemu, ya kuma zaba mana MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI. Ashe ba karamin yini bane wajen daraja. Idan kuwa haka ne, kana ina ake bidirin kyawawan ayyuka tun farkon wannan wata mai alfarma? Maza ka shigo cikin tawaga ka kwashi naka rabo. Mai bayarwa CIKAKKEN MAWADACI ne; duk yawanku yana iya baku ba tare da taskarsa ta nakasa ba.

6. YININ ARAFAH yini ne na tsantsar ikhlasi. Share harabar zuciyarka daga dukkan wata shakka, da shubuha, da riya; wadannan shara an daina yayinsu tun bayyanar Manzon Allah (SAW). Maza share zuciyarka, goge ta fyas, duk yanar dake jikin bangonta ka kankare. Aikin lada kwaya daya a cikin wannan yini na iya zama sanadiyyar dacewarka da mafi girmar ni’imar Ubangiji a kiyama.

7. Magabata basu yi kasa a gwiwa ba wajen ciyarwa, da tufatarwa, da ‘yantawa, da karantawa, da furtawa, da kuma rokawa cikin wannan YINI NA ARAFAH. Hakeem Bin Hizaam, daya ne daga cikin dattawa cikin Sahabban Manzon Allah (SAW). A daya daga cikin yinin Arafah da ya halarta bayan wafatin Manzon Allah, ya taba zuwa da rakuma 100 wadanda zai yi hadaya dasu, da kuma bayi 100, wadanda nan take a filin Arafah ya ‘yanta su don neman yardar Allah. Sauran mahajjata na ganin haka suka fashe da kuka, suka daga hannayensu sama suna cewa: “Ya Allah, kamar yadda wannan bawa naka ya ‘yanta wadannan bayi, mu ma ka ‘yanta wuyayenmu daga wuta.” A nasa bangare, Abdullahi dan Umar ya taba zuwa filin Arafah da bayi 1000, ya ‘yanta su a wajen nan take; don neman yardar Allah. Ina kake?

8. YININ ARAFAH yini ne na kyautata zato ga Ubangiji. Yini ne na kara kaimi wajen kyawawan ayyuka. Yini ne da duk wanda ya ke riya cewa Allah bazai yafe masa ma ba, to ya tabe. Abdullahi bn Mubaarak yace: “Na zo wajen Sufyan Ath-Thawri a yammacin Arafah, na same shi a kan gwiwowinsa yana ta addu’a.  Sai na taba kafadarsa. Yana waigowa sai na ga idanunsa cike da kwalla. Sai nace masa: ‘Shin, waye marashin arziki a wannan yini ne?” Nan take yace mini: “Wanda ke zaton Allah bazai yafe masa ba a wannan yini.” ALAHU AKBAR!

A KARSHE:  Mu yawaita mafificiyar zikiri wacce Manzon Allah yace ita ce addu’ar da yayi mafificiya, wacce kuma sauran Annabawa suka yi a gabaninsa a yini makamanciyar wannan:

LAA ILAAHA ILLAL LAAHU WAHDAHU LAA SHAREEKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMD, WA HUWA ALAA KULLI SHAI’IN QADEER!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: