Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYan bindiga sun sace DPO yan sanda Ibrahim Ishaq sun nemi N50m...

Yan bindiga sun sace DPO yan sanda Ibrahim Ishaq sun nemi N50m kudin fansa

Daga Muryoyi

Rahotanni daga jihar Edo na bayyana cewa yan bindiga sunyi garkuwa da shugaban yan sanda (DPO) na Fugar dake karamar hukumar Etsako, Ibrahim Ishaq kuma sun nemi Miliyan 50 kudin fansa.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito an sace DPO ne da yammacin ranar Juma’a tare da mai tsaron lafiyarsa amma mai tsaron lafiyar tashi ya kubuta daga baya. Lamarin ya faru a Ise river ta garin Auchi –  Ekperi-Agenebode jihar Edo.

Kwamishinan yan sanda na jihar Edo Philip Ogbadu ya tura gamayyar jami’an yan sanda zuwa yankin domin kubutar dasu.

- Advertisement -

Ishaq wanda dan asalin Ilorin ne dake jihar Kwara, ya rike DPO a jihar Kano kafin daga bisani aka mayar dashi Edo.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: