Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuYan ta'adda sun san yin NIN zai kawo masu babban cikas shi...

Yan ta’adda sun san yin NIN zai kawo masu babban cikas shi yasa suka taso ni gaba –inji Pantami

Daga Muryoyi

Minstan sadarwa da tattalin arziki zamani na Nigeria, Prof. Ibrahim Pantami, yace yin lambar shaidar zama dan kasa ta NIN ce kadai babbar hanya da Gwamnati zata bi domin shawo kan matsalar tsaro a Nigeria

Pantami ya bayyana cewa sanin tasirin da NIN ke da shi wajen dakile ayyukan ta’addanci shi yasa wasu yan ta’adda ko masu alaka da ta’addancin suka yi masa ca, suka rika kawo masa cikas kala-kala tare da yada farfaganda har ta kai ga sun maka Gwamnatin tarayya a kotu suna neman kada a aiwatar dashi.

Muryoyi ta ruwaito Pantami wanda ke bayanin haka a wajen wani lakca da yayi a Gombe yace babu kasar da zata iya cigaba ba tare da kididdiga ba, Ministan ya kawo misali da kasar Amurka da Ingila inda yace ba zaka iya shiga kasar ba sai ka samu shaidar “Social Security Number” da National Insurance Number kwatankwacin NIN a Nigeria.

- Advertisement -

Pantami ya ce a lokacinda yazo ya tarar a cikin shekara 13 mutum miliyan 42 kacal akayiwa rajista amma da zuwansa yanzu adadin masu shaidar NIN sun haura mutum miliyan 67

Muryoyi ta ruwaito Ministan ya ce muddin aka tattara lambar NIN to Gwamnati da hukumomin tsaro zasu iya bin kowane irin diddigin dan kasa da suke so. “Ba zan fallasa matakan da muke shirin dauka ba don kada in kawo wa shirin tsaro cikas amma dai muna nan muna tsara wata dabara tare da hadin guiwar hukumomi daban-daban da zamuyi amfani da hanyoyin zamani wajen kawo karshen matsalar tsaro”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: