Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba Su“Yanzu nine uban ku” -El-Rufai ya fadawa iyalan margayi Bantex cikin kuka

“Yanzu nine uban ku” -El-Rufai ya fadawa iyalan margayi Bantex cikin kuka

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sharbi kuka a lokacinda yake jawabin bankwana ga iyalan tsohon mataimakinsa Barnabas Bala Bantex a gidan Gwamnatin jihar Kaduna

El-Rufai yayi jawabai masu ratsa zuciyata na yabo da bayyana wasu kyawawan halaye na tsohon mataimakin Gwamnan wanda ya rasu makon da ya gabata kuma ake shirin bizne shi.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnan wanda kuka ya kwace masa yana tsakiyar jawabi ya bukaci iyalan tsohon mataimakin nasa su zo gareshi ga duk wata damuwa ko bukata tasu “Banex amini ne gareni tun a makaranta har zuwa kasuwanci da sha’anin Gwamnati, lallai nayi rashin babban aboki kuma amini nagari, don haka yanzu na zama uba gareku (iyalan Bantex) ku zo gareni kan duk wata bukata taku” nan kuka ya kwacewa Gwamnan

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: