Gwamnatin jihar Sokoto zata kafa hukumar Hisbah domin dakile yaduwar barna a fadin jihar
Daga Muryoyi
Gwamnatin jihar Sokoto ta gabatar da wani kuduri da zai bata damar kafa hukumar Hisbah a jihar
- Advertisement -
Gwamnatin ta ce tuni an fara shirye-shiryen sanya hukumar Hisbah a dokar jihar domin su rika taya sauran hukumomin tsaro aiki a jihar
Sarkin Musulmi ne dai zai zama uban hukumar a yayinda za a rika nada Kwamandan hukumar a hukumance a jihar. Yan sandan Hisban zasu rika aikin gyaran tarbiyya, yaki da rashin da’a da sutura da sauran ayyuka makamantansu