Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuZulum yace har da Jarirai cikin ma'aikatan bogi da aka kama a...

Zulum yace har da Jarirai cikin ma’aikatan bogi da aka kama a Borno ana biyansu 19M duk wata

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce an kama sunayen jarirai a cikin jerin maikatan bogi da aka kama a jihar bayan wani tantance ma’aikata da yasa akayi.

Gwamnan ya ce a karamar hukumar Shani kadai bayan sunayen jarirai da aka samu an kuma kama wani gida da suka sakala sunayen ma’aikatan bogi har 300 kuma ake biyansu albashi da alawus akalla miliyan 19 a duk wata

Zulum wanda ke jawabi a wajen bikin gargajiya na Menwara Cultural Festival da ya gudana ranar Asabar a garin Shani ya nuna takaicinsa “ace gida daya tal suna karbar albashin ma’aikata 300 kuma wai a haka ne al’ummar Shani suka fito zanga-zangar basa so ayi tantance ma’aikata”

- Advertisement -

Gwamna Zulum ya kara bankado wata badakala da ake yi a jihar ta Borno inda yace a karamar hukumar Shani an bankado yadda manyan jami’an garin suke sayar da guraben ayyuka da aka ware wa yan karamar hukumar akan kudi Naira dubu 250, suna sayarwa yan wasu garuruwan.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: