Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuShugaban Hafsan sojojin kasar India da matarsa da wasu 12 sun mutu...

Shugaban Hafsan sojojin kasar India da matarsa da wasu 12 sun mutu a hadarin jirgin sama

Daga Muryoyi

Wani jirgin soji dauke da Shugaban Hafsan Soji na kasar India General Bipin Rawat da matarsa Madhulika Rawat yayi hatsari a wani daji dake kusa da kauyen Coonoor a jihar Tamil Nadu,

Muryoyi ta ruwaito jirgin na fadowa kasa ya kama da wuta lamarin da ya jawo mutuwar akalla manyan sojoji 13 dake rakiyar Shugaban Sojojin.

Jirgin mai lamba IAF Mi-17V5 ya yi hadari da a yau bayan ya tashi daga filin jiragen saman sojojin kasar zashi wata kwalejin horas da sojoji ta kasar

- Advertisement -

Ana dai ganin shugaban hafsasn sojin General Bipin Rawat, babban na hannun daman Fraiminista kasar ne PM Narendra Modi, tuni dai Framinstan da ministan harkokin cikin gida, Amit Shah, da ministan tsaro Rajnath Singh suka mika ta’aziyyarsu

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: