Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn rasa rai wasu sun jikkata a gobarar da ta tashi a...

An rasa rai wasu sun jikkata a gobarar da ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar jahar Taraba

Daga Muryoyi

Akalla Daliba daya ta mutu kana wasu dalibai mata da dama sun jikkata a wata gobara da ta tashi a dakin kwanan dalibai mata na jami’ar jihar Taraba.

Muryoyi ta tattaro lamarin ya faru a daren ranar Juma’a a dakin wata daliba wacce ke tsakiyar barci sakamakon ta yi karatun jarabawa ta gaji

Majiyoyi sun ruwaito ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar, inda wani soket ya kama da wuta kafin a ankara hayaki ya turnike dakin dalibar wacce ke bacci sannan wuta ta haura katifar da take a kwance

- Advertisement -

“Dakyar dalibai mata da jami’a tsaron makarantar suka balle dakin suka yita kokari har aka samu aka kashe wutar kana aka fito da dalibar amma bayan an kaita asibiti Likitoci suka ce ta mutu sakamakon kunar da wutar tayi mata” inji wata ganau a lamarin

A bidiyon da Muryoyi ta kalla an jiyo daliban na salati “innalillahi wainna ilaihi rajiun” suna faman kokarin ciro dalibar a yayinda wasu ke ihun “yesu” bayan da aka gano wacce abun ya rutsa da ita sunan ta Enuseh Lawi daga karamar hukumar Donga jihar Taraba kuma ajinta 100 Level taba karantar ilimin safa da yawon bude idanu a jami’ar.

Daraktan yada labarai na Jami’ar Sa’ad Mohammed da Kakakin rundunar yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi sun tabbatar da faruwar lamarin. Kuma ana bincike akai domin kiyaye faruwar irin haka a anan gaba.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: