Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuGwamna Bala Mohammed Ya Ƙaddamar Da Kwamiti Kan Masarautar Sayawa

Gwamna Bala Mohammed Ya Ƙaddamar Da Kwamiti Kan Masarautar Sayawa

Daga Lawal Muazu Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya ƙaddamar kwamiti na musamman kan duba rahoton inganta zaman lafiya, bunƙasa tattalin arziki ,haɗin kai da kuma batun masarautar Sayawa.

Yayin ƙaddamar da kwamitima gidan gwamnati, Gwamna Bala ya shafe tsawon lokaci yana bitar tarihin rikici da rahotannin gwamnatocin da tuna gabata kan yankin kana yace kimanin shekaru talatin da suka shuɗe an yi shirye-shirye na musamman ciki har da na kwamitin gwamnatin tarayya kan zaman lafiyar yankin.

Ya ƙara da cewa ƙirƙirar masarautar sayawa daga ta Bauchi zai tallafawa shirin gwamnatinsa na inganta zaman lafiya da haɓaka tattalin arzikin al’umar yankin.

- Advertisement -

Lawal Muazu Bauchi mai tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani ya ruwaito  Gwamna Bala ya ƙara da cewa kwamitin na da makonni shida domin miƙa rahoton sa ga gwamnati don nazartar shawarwari.

Daga nan sai yayi kira ga kwamitin da ke da Ambassador Jibrin Dada Chinade a matsayin shugaba da yayi aiki da kwararru da masu ruwa da tsaki don tabbatar da nasarar aikin dake kan su.

A cewar Gwamna Bala ayyukan kwamitin sun haɗa da laluɓo musabbabin rigingimu da hanyoyin magance su, tattauna batun samar da masarautar sayawa da haɗa kan al’umar Tafawa Balewa, Ɓogoro da kuma Dass.

Lawal ya ruwaito Sauran ayyukan kwamitin sun haɗa da hanyoyin daƙile rikicin addini ko ƙabila, kafa iyakoki da sauran su.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: