Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAbdul’aziz Yari Shi Ya Fi Cancanta Da Zama Shugaban Jam'iyyar APC Na...

Abdul’aziz Yari Shi Ya Fi Cancanta Da Zama Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa

  1. Ra’ayin Engr (Dr.) Abdullahi A. Tsafe

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari na cikin jam’iyyar adawa tun da aka dawo da mulkin farar hula a 1999. Tun lokacin jam’iyyar APP Yari bai sauya sheka ba har zuwa ANPP, har ta kai ga ya zama shugaban jam’iyya na jihar Zamfara, kuma sakataren kudi na jam’iyyar a matakin kasa.

Wata kungiyar magoya bayan tsohon Gwamnan mai suna ‘Support A.A Yari For APC National Chairman 2021’ wadda take da burin ganin Yari ya zama shugaban jam’iyyar ta APC a matakin kasa, ta zayyano wasu kwararan hujjojin da ya kamata a ce Yari ne zai jagoranci jam’iyyar.

Kungiyar ta kara da cewa, a shekarar 2003 ya nemi takarar memba na majalisar tarayya mai wakiltar Anka/Maradun, kuma ya fito takarar gwamna na ma ya ci.

- Advertisement -

A shekarar 2014 a yayin shirye-shiryen zaben 2015, Yari na daga cikin hazikan mutane 11 da suka kirkiro jam’iyyar APC.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2000, Yari yana daga cikin mutane bakwai da suka gana da shugaba Buhari domin kwadaita masa shiga harkar siyasa tare da neman ya fito takarar shugaban kasa. Inda bayan Buhari ya ki amincewa da tayin, sai suka gayyato wasu na jikinsa irin su marigayi AVM Muktar Muhammad domin su sa baki kan lamarin, inda bayan bayan shiga lamarin da su persuade Buhari, on AVM da su Buba Galadima, Naja’atu Muhammad, marigayi Kumo, Sule Hamma da Fatima Muhammad, sai shugaba Buhari ya karbi tayin.

Irin wannan dogon tarihi da Yari yake da shi a siyasa a matakin kasa da jiha, ana ganin hakan zai iya ba shi damar kayar da dukkanin abokan takararsa, wadanda ba su da irin wannan tarihin a matakin siyasar kasa.

Wani kwarin gwiwar da Yari yake da shi shine irin tarihin da yake da shi a jam’iyyar, inda yana daya daga cikin mutane sha daya da suka kirkire ta kuma suka jawo hankulan ‘yan siyasar yankin kudu har aka samu nasara.

Haka kuma Yari ya soma siyasa ne tun daga tushe, inda har ya zama Gwamna, wanda hakan ya nuna cewa zai iya rike duk wani matsayi a siyasance.

Idan muka waiwayi salon mulkinsa a lokacin da yake Gwamnan Zamfara kuma, Yari ya yi matukar taka rawar gani musamman a bangaren tsaro. Domin yakan yi kokarin toshe matsaka tun kafin afkuwarta.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: