Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAiki mai tsoka: Dangote zai dibi sabbin ma'aikata

Aiki mai tsoka: Dangote zai dibi sabbin ma’aikata

Daga Muryoyi

Kamfanin Dangote ya soma karbar sunayen dalibai masu hazaka da suka kammala da “First Class” ko “Second class (2:1)” domin daukarsu aiki a sabuwar matatar mansa wato Dangote Refinery

Muryoyi ta ruwaito kamfanin yace ya tura takardu ga jami’o’in Najeriya 25 yana neman su aiko masa da sunayen daliban da suka kammala karatu daga shekarar 2019 da 2020 da kuma 2021 amma yace zasu dibi daliban da shekarunsu ke kasa da 30 ne kawai.

Sanarwar ta ce za dibi daliban da suka karanci musamman Engineering da chemical, da mechanical, da electrical, da kuma electrical/electronics engineering daga sanannun jami’o’in Najeriya ciki har da su Polytechnic

- Advertisement -

Kakakin kamfanin Mista Anthony Chiejina ya shaidawa majiyar Muryoyi cewa duk daliban da aka diba za a tantance su kana a tura su kasashen waje domin suyi kwas

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: