Daga Muryoyi
Jarumar fina-finai ta Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta nuna bacin ranta game da yawan kashe-kashe da ake yi a Nigeria musamman anan yankin Arewa.
Muryoyi ta ruwaito a wani gajeren sako da ta rubuta a shafin ta na Facebook, Jarumar ta yi Allah ya isa kan wannan kashe-kashe da ake yi mana kuma babu mai iya tsawatawa.
Gabon ta ce “Yaro daya aka kashe a Lagos an fita nemar masa hakkinsa, ba maganar jam’iyya ko addini ko jinsi, amma mu ana ta kashemu an rasa ko masu magana, Allah ya saka mana”
- Advertisement -
Kashe-kashe na baya bayan nan dai shine na wasu matafiya kusan 40 da yan bindiga suka cinnawa wuta suka kona su kurmus